
Peter Obi







Tsohon ɗan takarar shugaban kasa, Mista Peter Obi ya buɗe shafin TikTok, ya samu mabiya mutane sama da 6,000 cikin ƴan sa'o'i, ya wallafa bidiyo mai ɗauke da saƙo.

Kungiyar matasan yankim Neja Delta ta bayyana goyon bayanta ga shirin haɗakatar tsohon ɗan takarar shugaban kasa, Peter Obi da Gwamna Bala na Bauchi.

Rahotanni daga fadar gwamnatin jihar Bauchi sun nuna cewa nan ba da jimawa da Peter Obi zai fice daga LP zuwa jam'iyyar PDP a shirye-shiryen 2027.

Nasir El-Rufa'i ya bayyana cewa yana fatan Atiku Abubakar da Peter Obi za su hadu da shi a SDP domin tunkarar Bola Tinubu a zaben 2027 domin kayar da APC.

Yayin da aka fara shiri ta karkashin kasa game da zaben 2027, jam'iyyun adawa a Najeriya sun yunkuro domin kokarin tumbuke Bola Ahmed Tinubu daga mulki.

Gwamna Bala ya ce yana shirye ya yi aiki da Peter Obi domin karfafa adawa a gabanin 2027, yayin da Obi ya jaddada cewa talauci ne tushen matsalar rashin tsaro.

Tsohon gwamnan jihar Anambra kuma ɗan takarar shugaban kasa na LP a zaben da ya gabata na 2023 ya shiga ganawar sirri da Gwamna Bala Muhammed a Bauchi.

Shugabar riko na LP, Sanata Nenadi Usman ta karyata jita-jitar cewa ta fice daga jam’iyyar zuwa jam’iyyar SDP mai adawa a Najeriya wanda Nasir El-Rufai ya koma.

Bayan rasa Nasir El-Rufai, hadimin shugaba kasa, Daniel Bwala ya ce dan takarar shugaban kasa a LP, Peter Obi zai bar jam'iyyarsa ya koma APC kafin zaben 2027.
Peter Obi
Samu kari