
Jihar Plateau







Marigayi Sheikh Saidu Hassan Jingir ya taba musuluntar da kabilar Cakobo baki daya, dukkan mutanen kabilar da sarkinsu. Malamin ya fara karatu wajen mahaifinsa.

Rundunar 'yan sandan Najeriya a Filato ta karyata cewa akwai kasuwar da ake sayar da sassan jikin dan Adama a jihar. An gargadi iyaye kan tarbiyya.

Rasuwar Sheikh Saidu Hassan Jingir ta girgiza malamai da yan siyasa. Sheikh Daurawa, Isa Ali Pantami, gwamnoni da sauran yan siyasa sun yi ta'aziyya.

Mataimakin shugaban malaman kungiyar Izala Sheikh Saidu Hassan Jingir ya rasu bayan fama da jinya da ya yi. Malamin ya rasu a jihar Filato a azumi.

Rundunar yan sanda ta kaddamar da bincike bayan mutuwar wani jami'inta mai muƙamin sufata da aka farmaka a Jos da ke jihar Plateau a Arewacin Najeriya.

Wasu tsagerun 'yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun hallaka jami'an 'yan sanda. 'Yan sandan sun rasu ne yayin wani artabu da suka yi.

Barista Kusamotu ya ce Gwamna Mutfwang ba shi da ikon hana hakar ma’adinai a Filato, yana mai cewa wannan mataki ya sabawa kundin tsarin mulkin kasa.

Dakarun sojojin Najeriya sun kashe ‘yan bindiga biyu, sun kama wasu a Filato, tare da ceto wata mata da ‘yarta ba tare da sun ji rauni ba. Ana ci gaba da kai samame.

Hon. Ahmed Idris Wase ya nuna kin amincewa da mayar da cibiyar bincike ta FIIRO zuwa jihar Legas. Wase ya bukaci 'yan majalisa su ki amincewa da kudirin.
Jihar Plateau
Samu kari