Muhammadu Buhari
Tsohon Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya jajanta wa Bola Tinubu kan turmutsitsin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane a jihohin Najeriya a wannan mako.
Tsofaffin shugabannin kasa a Najeriya za su samu N27bn a shekarar 2025 da aka ware domin biyansu hakkokinsu tare da mataimakansu lokacin mulkinsu.
Bayan kwace filayen Muhammadu Buhari da yan siyasa, Ministan Abuja, Nyesom Wike ya ba da wa'adin mako biyu ga wadanda abin ya shafa da su biya kudin da ake bukata.
Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya mayar da martani ta bakin kakakinsa, Garba Shehu inda ya ce ba mai gidan nasa ba ne ya siya filin da hannunsa.
Minista Wike ya kwace filaye 762 a Maitama, Abuja, ciki har da na Buhari, bisa rashin biyan haraji; masu filaye 614 na da wa'adin makonni biyu su biya.
Dan takarar shugaban kasa a zaben 2023 kuma dan gwagwarmaya, Omoyele Sowore, ya sha suka bayan ya yi kalamai masu kaushi a kan Buhari a ranar haihuwarsa.
Tsohon hadimin shugaban kasa, Femi Adesina ya ce Muhammadu Buhari mutumin kirki ne, ya na gudun duk wani abu da zai kara jefa talaka cikin wahala.
Solomon Arase ya ce Buhari ginshiki ne na haɗin kai, tare da gode masa kan jajircewarsa wajen tsaro, yaki da cin hanci da kuma tabbatar da cigaban Najeriya.
Alhaji Aliko Dangote da tsohon sakataren gwamnati, Boss Mustapha, sun ziyarci tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari yayin da yake bikin cika shekaru 82 a Daura.
Muhammadu Buhari
Samu kari