Siyasa
Jam'iyyar APC ta kafa kwamitin sulhu a jihar Adamawa domin warware rikicin cikin gida da ya barke a jam'iyyar. APC ta bukaci hadin kai kafin zabe mai zuwa.
Magoya bayan APC sun fara rokon ministan harkokin tattalin arzikin ruwa, Oyetola ya sake komawa ya nemi takarar gwamnan jihar Osun a zaɓen 2026 da ke tafe.
Sarkin Onitsha watau Obi na masarauyar Onitsha ya ce ya kamata Najeriya ta gwada mace a kujerar shugaban ƙasa, ya ce an yi gwamna mace a jihar Anambra.
Jam'iyyar LP da Peter Obi ke jagoranta da fara shirin karfafa shugabanci a jihohin Najeriya 36. A ranar Juma'a LP za ta kaddamar da shugabanni a jihohi.
Kungiyar Team New Nigeria (TNN) ta fara sanya fastocin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a birnin Kano. Kungiyar na bukatar ya yi takara a zaben 2027.
Babbar Kotun da ke jihar Rivers da rusa matakin dakatar dan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar Andoni-Opobo/Nkoro mai suna Awaji-Inombek Abiante.
Kudirin sauya fasalin harajin Shugaba Bola Tinubu na ci gaba da samun tangarɗa musamman a Arewacin Najeriya, mun haɗa maku ƴan siyasar da suka yi raddi.
Kusa a APC reshen Kano ya caccaki gwamnatin Bola Tinubu. Ya zargi gwamnatin tarayya na jefa jama'a a cikin masifa. AbdulMajeed Danbilki Kwamanda ne ya fadi haka.
Majalisar dokokin jihar Kano ta buƙaci sanatoci da ƴan majalisar wakilai na tarayya su haɗa kai su yaƙi sabon kudirin sauya fasalin harajin Bola Ahmed Tinubu.
Siyasa
Samu kari