Shugaban kasaz Bola Tinubu ya gana da gwamnonin APC a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, yayin da jam’iyyar ke ƙara shirye-shiryen tunkarar zaɓen 2027.
Shugaban kasaz Bola Tinubu ya gana da gwamnonin APC a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, yayin da jam’iyyar ke ƙara shirye-shiryen tunkarar zaɓen 2027.
Tsohon minista, Abubakar Malami ya kaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen ADC mai mambobi sama da 600 a Kebbi, inda ya buƙaci haɗin kai da kamfen cikin lumana.
A labarin nan, za a ji cewa Baffa Babba Dan Agundi, jigo a jam'iyyar APC da ke Kano ya yi magana game da yadda sauya sheƙar Gwamna Abba Kabir Yusuf ta taimaki Kano.
Jam’iyyar APC ta lashe kujerar shugabancin Kuje a zaben kananan hukumomin Abuja, inda Danjuma Shekwolo ya samu kuri’u 17,269, ya doke PDP da jam'iyyar APGA.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yabawa Ministan Abuja, Nyesom Wike, kan rawar da ya taka a nasarar APC a zaben kananan hukumomi shida da aka gudanar.
Hukumar zabe INEC ta sanar da sakamakon zaben AMAC a Abuja, inda APC ta tabbatar da nasarar Christopher Maikalangu da kwarin gwiwar zaben shekarar 2027.
Aliyu Nabil da Aminu Sa'ad na APC sun lashe zaɓukan cike gurbi a Kano da aka gudanar ranar Asabar 22 ga Fabrairu, 2026. An samu ƙarancin fitowar jama'a.
Daniel Nuhu na APC ya lashe zaɓen Kwali da ƙuri'u 17,032 a zaben ranar Asabar, 22 ga Fabrairu, 2026. Ya doke PDP a zaɓen ƙananan hukumomin Abuja.
Dan Anambra, Edwin Chukwujekwu ya zama Mataimakin Sakataren APC a Gombe, yana mai jaddada haɗin kai da adalci da inganta dimokuraɗiyya cikin jam'iyya.
Joshua Ishaku na APC ya lashe zaɓen Bwari da ƙuri'u 18,466 a zaben da aka gudanar ranar 21 ga Fabrairu, 2026. Ya doke ADC da ZLP bayan janyewar ɗan takarar PDP.
Mohammed Kasim na PDP ya lashe zaɓen Gwagwalada da ƙuri'u 22,165, inda ya doke APC a zaɓen ƙananan hukumomin Abuja da aka gudanar ranar 21 ga Fabrairu, 2026.
Siyasa
Samu kari