Abin Duniya Abin Banza Ne, Ku Rike Amana: Shugaba Buhari
- Shugaba Buhari ya bayyana cewa lokacin 'kankani ya rage ya sauka daga mulki ya koma gida
- Shugaban kasan ya ce ko fuloti na fili guda bai da a wajen Najeriya, abin duniya bai damesa ba
- Saura watanni biyar shugaban kasan ya kare wa'adinsa na biyu kan karagar mulkin Najeriya
Damaturu - Shugaba Muhammadu Buhari ya yi kira ga al'ummar jihar Yobe su zabi duk shugaban da suke so kuma su rike amanar da Allah ya daurawa kowanne daga cikinsu.
Buhari ya bayyana hakan ne yayinda ya halarci taron yakin neman zaben jam'iyyar All Progressives Congress APC da ya gudana ranar Talata, 10 ga Junairu, 2023 a Damaturu.
Shugaban kasan ya bada tarihin yadda aka yi masa wulakanci iri-iri lokacin da yake neman shugabancin kasar Najeriya.
Ya ce shi ko kadan abin duniya bai damesa ba kuma nan da dan 'kankanin lokaci zai sauka daga mulki ya koma gida.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Yace:
"Ni na tashi maraya, ban san mahaifi na ba. Kuyi iyakan kokarinku ku biya amanar da aka baku da ta iyalin ku."
"Abin duniya abin banza, ku rike amana, ku rike jama'ar da ke karkashin ku."
"Na shekara 80, na yi aikin soja, na yi na ofis, na shiga siyasa, na nemi shugaban kasa sau uku, na shiga shari'a na ce a tausaya min, sai aka min dariya"
"Mu mun gama namu Insha'aLLahu, nan da wata biyar zamu koma gida."
Ku yi noma, Buhari ya yi kira ga al'ummar Yobe
Shugaban kasan ya bayyana cewa idan lokacin damina yazo, mutane su fita noma don samun abinci. Hakazalika idan rani yazo su nemi aikin yi.
A cewarsa:
"Ina son ku maida hankali idan Allah ya kawo damina ku noma abinda zaku ci. Idan damina ta wuce ku samu sana'ar da zaku yi."
Asali: Legit.ng