Ortom Bai Fadi Gaskiya Ba, Kwamitin PDP Bata kada Kuri’a Akan Daukan Abokin Takara na ba - Atiku
- Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP ya ce kwamitin da aka kafa don ba da shawarar daukar abokin takararsa bai gudanar da zabe ba
- Jam’iyyar PDP ta fada cikin rikici tun da Atiku ya zabi Ifeanyi Okowa, a matsayin abokin takararsa a zaben shugaban kasa na 2023.
- Gwamna Samuel Ortom, ya ce 14 daga cikin 17 na mambobin kwamitin ba da shawarar daukar abokin takara sun fifita Wike a kan Okowa
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - A halin yanzu, mun fahimci cewa wanda zai rike kujerar takarar Mataimakin Shugaban kasa ya zama abin rigima a PDP, manyan na-kusa da Gwamna Wike sun ja daga.
Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, ya ce kwamitin da aka kafa don ba da shawarar daukar abokin takararsa bai gudanar da zabe ba.
Abubakar ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da tashar talabijin ta Arise a ranar Juma’a.
Jam’iyyar PDP dai ta fada cikin rikici ne tun bayan da Atiku ya zabi Ifeanyi Okowa, gwamnan Delta a matsayin abokin takararsa a zaben shugaban kasa na 2023.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Akwai kuma rahotannin da ke cewa galibin mambobin kwamitin da aka kafa don ba da shawarar abokin takarar sun zabi Wike.
Samuel Ortom, gwamnan Benue, ya ce 14 daga cikin 17 na mambobin kwamitin ba da shawarar daukar abokin takara sun fifita Wike a kan Okowa.
Atiku ya ce
“Kwamitin ta gabatar mun da sunayen guda uku in zaba daya daga cikin su, amma ba su kada kuri’a ba.
"Bugu da kari, Ortom da kansa ya jagoranci wannan kwamiti, ya san cewa ba a kada kuri’a ba kuma ina da rahoton kwamitin.
Da aka tambaye shi ko Ortom ya yi wa jama’a karya, Abubakar ya mayar da martani:
“Abin da ya ce ba daidai ba ne, zan iya ba ku kwafin da aka aiko mini, ba a yi zabe ba kwata-kwata.
Atiku: Banyi Watsi Da Wike Ba, Na zabi Dan Takarar Da Zan Iya Aiki Da Shi ne
A wani labari kuma, Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce bai zabi Nyesom Wike, gwamnan Rivers, a matsayin abokin takararsa ba, saboda yana son wanda zai yi aiki da shi cikin aminci.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da yayi da Arise TV ranar Juma'a
Asali: Legit.ng