Tarihin ‘Dan takaran Yobe da ya karya lakanin Ahmad Lawan, ya sa shi yin biyu-babu
- Da alama Bashir Sherrif Machina ne zai yi wa jam’iyyar APC takara a 2023 a yankin Arewacin Yobe
- Hon. Bashir Sherrif Machina ya taba zama ‘Dan majalisar wakilan tarayya a jam’iyyar SDP tun a 1992
- Kafin abubuwa su canza, Machina Mai gidan Gwamna Mala Buni ne a lokacin su na jam'iyyar ACN
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Yobe - Hon. Bashir Sherrif Machina ya zama ‘dan majalisar wakilan tarayya ne a 1992. Daily Trust ta ce a lokacin ya na mai shekara 20 da ‘yan kai a Duniya.
Bashir Sherrif Machina ya wakilci mazabun Karasuwa, Nguru, da Machina, Yusufari na yankin jihar Yobe a majalisar tarayya a karkashin jam’iyyar SDP.
Jaridar ta bi diddiki domin bankado tarihin ‘dan takaran Sanatan na Arewacin jihar Yobe a 2023.
Sai shekaru bakwai bayan Sherrif Machina ya je majalisa, sannan Ahmad Lawan ya lashe zabe domin ya wakilci mutanen shiyyar Bade da Jakusko a APP.
Lawan ya ci taliyar karshe?
Da ya shafe wa’adi biyu watau shekaru takwas a majalisar wakilai, sai Lawan ya zama ‘dan majalisar dattawa a Mayun 2007, har yau yana kan mulki.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Sai a zaben fitar da gwani na jam’iyyar APC da aka yi na wannan shekara sannan shugaban majalisar ya sha rasa tazarce, ya tafi neman shugaban kasa.
A lokacin da Lawan yake harin zama ‘dan takarar shugaban kasa a APC, Basheer Machina, ya shiga zaben tsaida gwani na Sanatan yankin Arewacin Yobe.
Machina ba na yau ba ne a siyasa
Rahoton da jaridar ta fi ya bayyana cewa Hon. Machina tsohon Mai gidan Gwamna Mai Mala ne. Hakan ta sa watakila ya samu takara ba tare da hamayya ba.
Da yake wakiltar mutanensa a 1992 kafin gwamnatin soja su ruguza majalisa, Machina yana da shekara 26 ne, ya rike shugabancin kwamitin takin zamani.
Basheer Machina ya shiga siyasa ne a dalilin tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Ambasada Babagana Kingibe, wanda shi ne sanadiyyarsa na shiga PDP.
Duniya juyi-juyi
Tsohon ‘dan majalisar ya yi shekaru kusan hudu a PDP har ya rike mataimakin mai binciken kudi na kasa. A daidai lokacin ne Dr. Ahmad Lawan ya zama Sanata.
Da Machina yake ‘dan majalisa shekara 30 da suka wuce, shi kuma Mala Buni Kansila ne a kauyensa a Buni. A hankali har ya zama shugaban ACN na jiha.
Ko da aka nada Buni a matsayin shugaban ACN na jihar Yobe a shekarun baya, Machina ya zama shugaban masu binciken kudi na jam’iyyar hamayyar na kasa.
A karshe dukkansu (Mala Buni da Bashir Machina) su ka sauya-sheka daga ACN zuwa CPC. Daga baya suka narke a APC da a karkashinta ne suka samu matsayi.
Asali: Legit.ng