Fasto ya gaji da yin addu’a, ya fito zai yi takarar Gwamna a karkashin jam’iyyar APC
- Rabaren Hyacinth Alia ya shiga siyasa da nufin neman takarar Gwamnan jihar Benuwai a zaben 2023
- Babban Faston zai yi takara a jam’iyyar APC mai mulki, ya ce lokaci ya yi da za a gyara Benuwai
- Hyacinth Alia yana cikin manyan jagororin mabiya katolika a yankin Gboko da ke jihar ta Benuwai
Abuja - Hyacinth Alia wanda babban limamcin cicin katolika ne a Najeriya, ya shiga sahun masu neman kujerar gwamnan jihar Benuwai a zabe mai zuwa.
Jaridar The Nation ta fitar da rahoto cewa Rabaren Hyacinth Alia zai tsaya takarar gwamnan Benuwai ne a karkashin jam’iyyar APC mai hamayya a jihar.
Hyacinth Alia ya sanar da nufinsa a ranar Asabar, 30 ga watan Afrilu 2022, a lokacin da ya zauna da jagororin wata kungiyar magoya bayansa, Alia Alliance.
Rahoton ya ce shahararren Faston ya yi zama da shugabannin wannan kungiya da ke taya shi yaki wajen ganawa da mutanen Benuwai da ke zama a Abuja.
Ba yau aka fara ba
Faston wanda shi ne babban limamin katokila a garin Gboko ya ce a shekarar 1992, Marigayi Rabaren Moses Adasu ya rike kujerar gwamna a Benuwai.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Idan ya zama gwamna a 2023, Alia ya ce zai maida hankali ne wajen kula da al’ummar Benuwai.
Manufofin Rabaren Alia
Mai neman shiga takarar ya jero abubuwa bakwai da zai yi idan ya kafa gwamnati. Daga ciki akwai bunkasa ilmi da kiwon lafiya da yaki da rashin gaskiya.
Kamar yadda jaridar PM News ta bayyana a rahoton da ta fitar, Faston ya kuma shaidawa jama’a cewa zai kawo zaman lafiya, tare da hana taba filayen jama’a.
Rabaren Alia ya na ganin cewa Benuwai ta dade ta na rashin sa’ar shugabanni, ya ce idan ya samu shugabanci zai dawo da martaba da darajar wannan jihar.
“Jihar Benuwai ta shiga wani irin mawuyacin hali, lokaci ya yi da za shawo kan matsalar jiha. Na shiga harkar siyasa domin in ceto daga durkushewa.”
- Rev. Fr. Hyacinth Alia
Shugaban kungiyar Alia Alliance, Peter Ashiekaa ya yi kira ga jama’a su goyawa Rabaren Alia baya domin ya zama gwamna da nufin ceto mutanen Benuwai.
Lawan a zaben 2023
A siyasar kasa kuma, dazu aka ji labari Ahmad Lawan wanda shi ne shugaban majalisar dattawa zai shiga yakin neman kujerar Shugaban Najeriya a zaben 2023.
Bayan shekaru kusan 23 a majalisar tarayya, ana rade-radin Sanata Lawan zai yanki fam da niyyar shiga zaben fitar da gwani na kujerar shugaban kasa a APC.
Asali: Legit.ng