Zaben APC: Goyon bayan Buhari, sanin siyasa da abubuwa 4 da suka taimakawa Adamu

Zaben APC: Goyon bayan Buhari, sanin siyasa da abubuwa 4 da suka taimakawa Adamu

  • A karshen makon da ya wuce Sanata Abdullahi Adamu ya zama shugaban jam’iyyar APC na kasa
  • Adamu shi ne shugaba na biyar da aka yi a jam’iyyar APC – Akande, Oyegun, Oshiomhole, da Buni
  • Amma wannan ne karon farko da wani ‘dan siyasar Arewa zai jagoranci APC (ba a rikon kwarya ba)

A wannan rahoto na yau, Legit.ng Hausa tattaro wasu dalilai da ake ganin sun taimakawa Abdullahi Adamu wajen samun wannan matsayi:

1. Ware yadda za a raba mukamai

Shugabannin APC sun yi tsari a kan yadda za ayi kason kujerun NWC, an kuma amince shugaban jam’iyya na kasa ya fito ne daga shiyyar Arewa maso tsakiya.

Wannan matsaya da aka cin ma ya sa aka ragewa Abdullahi Adamu aiki. Da farko akwai ‘Yan Arewa maso tsakiya da gabas da suka so su samu wannan kujera.

Kara karanta wannan

Duk da ‘Dan takararsa bai yi nasara ba, Tinubu ya taya Adamu murnar zama Shugaban APC

2. Goyon bayan Buhari

Bayan ware mukamai da aka yi a APC, goyon bayan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba Sanata Adamu ya yi tasari a zaben shugabannin da aka gudanar.

Gwamnonin jihohin APC 22 sun yi zama da Mai girma shugaban Najeriya, kuma ya nuna masu karara cewa yana tare da Adamu, hakan ta sa aka mara masa baya.

3. Gawurta a siyasa

Ganin cewa Muhammadu Buhari ya gama cin zamaninsa, APC ta na bukatar ‘dan siyasar da ya kware a 2023 don haka ne ta zakulo mutum irin Sanata Adamu.

Adamu ya taba rike shugabancin jam’iyyar NPN, ya yi Ministan tarayya, sannan ya yi shekaru 16 a kujerar gwamna da sanata, tun 1979 bai taba fadi wani zabe ba.

4. Bai da tsoro

Kara karanta wannan

Akwai yiwuwar Buhari ya dauko ‘Dan takaran da zai ba kowa mamaki, ya mara masa baya

Wani abu game da Turakin Keffi bayan zamansa kwararren ‘dan siyasa shi ne bai jin tsoron ya tunkari mutum, ya fada masa abin da yake tunanin shi ne gaskiya.

Zai yi wuya a samu tamkar tsohon gwamnan na Nasarawa a APC. Baya ga shaidar da aka yi masa na amana da biyayya, kusan babu wanda zai iya tankwara Adamu.

Zaben APC
Taron zaben jam'iyyar APC Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

5. Aikin kwamitin sulhu

Duk da cewa daga jam’iyyar PDP Abdullahi Adamu ya shigo APC, shi ba bare ba ne a APC mai mulki. Shi ne ya jagoranci kwamiti mai sasanta rikicin cikin gida.

Mai Mala Buni ya zabi Adamu ya yi wa fusatattun ‘ya ‘yan jam’iyya sulhu domin a dinke baraka. Wannan aikin da ya yi ya taimaka masa wajen karin samun fada.

6. Bai nemi mukami ba

Da farko Sanata Adamu bai cikin wadanda suka kwallafa rai wajen samun shugabancin jam’iyyar APC. Legit.ng Hausa ta fahimci sai daga baya ya shigo cikin lissafi.

Kara karanta wannan

Jerin shugabannin da suka yi nasara, da wadanda suka sha kasa a zaben jam’iyyar APC

Ganin bai da kwadayin shugabantar jam’iyyar, watakila hakan ya sa shugaba Muhammadu Buhari ya hakikance a kan shi ya kamata ya jagoranci APC bayansa.

7. An zabi shugabanni ta maslaha

Dalili na karshe da mu ke ganin ya yi tasiri wajen zaman Sanatan na Nasarawa shugaban APC na kasa shi ne yadda jam’iyya ta bi wajen fito da shugabannnin na ta.

Ba a kada kuri’a a wajen zaben jam’iyyar APC ba, an yi maslaha ne inda kowane ‘dan takara ya janye. Hakan ya taimakawa Adamu a kan duk abokan hamayyarsa.

Tinubu ya taya Adamu murna

A makon nan ne aka ji Asiwaju Bola Tinubu ya fitar da jawabi na musamman bayan an yi zaben shugabannin APC na kasa, ya na taya wadanda suka yi nasara murna.

A jawabin da jigon jam’iyyar mai mulki ya fitar, ya yabi sabon shugaban na sa Abdullahi Adamu, ya ce ‘dan siyasa ne irinsa mai jama'a, kuma wanda ya ga jiya da yau.

Kara karanta wannan

Mulki ya samu: Bidiyo ya nuna sabon shugaban APC na buga wasan dara da wani sanata

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng