Akwai yiwuwar Buhari ya dauko ‘Dan takaran da zai ba kowa mamaki, ya mara masa baya a 2023

Akwai yiwuwar Buhari ya dauko ‘Dan takaran da zai ba kowa mamaki, ya mara masa baya a 2023

  • Jam’iyyar APC mai mulki ta koma lissafin wanda zai rike mata tuta a zaben shugaban kasan 2023
  • A watan Mayu ne za a gudanar da zaben tsaida gwani domin fito da magajin Muhammadu Buhari
  • Watakila shugaban Najeriya ya zakulo wani bari a matsayin wanda za a ba tikitin jam’iyyar APC

Abuja - Bayan kammala zaben shugabanni na jam’iyyar APC mai mulki, hankali ya koma a kan wanda za a ba tuta a zaben shugaban Najeriya da za ayi.

Kamar yadda jaridar Vanguard ta kawo rahoto, za a shirya zaben fitar da gwanin ne a watan Mayu. A nan za a san wanda zai rikewa jam’iyyar APC tuta.

Kawo yanzu akwai mutane akalla tara da suke harin kujerar shugaban kasa a zaben na 2023.

Rahotanni na nuna cewa daga cikin wadanda ake tunanin su ne a gaba akwai Ministan sufuri, Hon. Rotimi Amaechi da gwamnan CBN, Godwin Emefiele.

Kara karanta wannan

Jerin shugabannin da suka yi nasara, da wadanda suka sha kasa a zaben jam’iyyar APC

Masu neman tikitin APC

Sauran sun hada da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Farfesa Yemi Osinbajo, Alhaji Yahaya Bello, Dr. Kayode Fayemi, David Umahi da kuma Sanata Rochas Okorocha.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rochas Okorocha da Bola Ahmed Tinubu su na cikin wadanda aka kafa jam’iyyar APC da su.

Shugabannin APC
Gwamnoni da sababbin shugabannin APC Hoto: @bashahmad
Asali: Facebook

Akwai yiwuwar APC za ta sake yin amfani da tsarin maslaha ne wajen tsaida wanda zai yi takarar shugaban kasa idan lokacin zaben fitar da gwani ya yi.

Wanene Magajin Buhari?

Kawo yanzu, babu wanda ya san inda Mai girma Muhammadu Buhari ya dosa. Babu ‘dan siyasar da zai iya cewa ga wanda shugaban kasa yake so ya gaje shi.

Jaridar ta ce babu mamaki Buhari ya zakulo wani daga gefe dabam, a damka masa tutar jam’iyyar APC. Hakan ya na nufin za ayi fatali da sanannin ‘yan siyasa.

Kara karanta wannan

Shugabancin 2023: Okorocha ya ce ya kamata Tinubu ya hakura ya bar masa tikitin APC

Wani daga cikin magoya bayan mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya ce zaman Abdullahi Adamu shugaban APC zai taimaka su samu tikiti.

Legit.ng Hausa ta zanta da wanda ya san Yemi Osinbajo, ya shaida mana zai yi wahala ya iya samun tikiti, kuma za a fuskanci kalubale a babban zaben badi.

Bayan shekaru bakwai, tsohon hadimin fadar shugaban kasan ya ce mutane su na ganin gwamnatin APC ba ta iya cika alkawarin da tayi wa talaka ba.

Shi dai sabon shugaban APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu ya yi alkawari zai yi gaskiya a zaben 2023 wajen ganin an fito da ‘dan takarar shugaban kasa.

An yi wa Buhari kafa a APC

A baya kun ji yadda ta kaya da shugaba Muhammadu Buhari, mataimakinsa Yemi Osinbajo da Asiwaju Bola Tinubu a zaben shugabanni na jam’iyyar APC.

Muhammadu Buhari da Bola Tinubu sun tsira da manyan kujeru daya a NWC, Gwamnoni kuma sun ci karensu babu babbaka, Kano ba ta da mukami mai tsoka.

Kara karanta wannan

An fitar da sunayen wadanda za su rike mukamai a APC, babu wasu ‘Yan takarar Buhari

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng