Zaben APC: An fitar da sabuwar sanarwa, masu rike da mukamai ba za su yi zabe ba
- Jam’iyyar APC ta ce babu wani wanda yake rike da kujerar siyasa da zai shiga zaben shugabanni
- Wata sanarwar kwamitin rikon kwarya da tsara zaben APC na kasa ta tabbatar da wannan daf da zabe
- An dauki wannan matsaya ne domin gudun abin da zai biyo baya saboda sabuwar dokar zaben 2022
Abuja - Jam’iyyar APC mai mulki ba za ta bar wadanda suke rike da kujerun siyasa wajen kada kuri’a a zaben shugabanni na kasa da za a gudanar ba.
The Cable ta ce wannan sanarwa ta fito ne a yammacin ranar Alhamis, 24 ga watan Maris 2022.
A wani jawabi da jam’iyyar ta fitar, ta bayyana cewa masu rike da mukaman gwamnati da aka zaba a matsayin masu kada kuri’a ba za su yi zabe ba.
Kwamitin CECPC ya bada dalilin daukar wannan mataki da cewa akwai ta-cewa game da dokar zabe na kasa, don haka aka hana masu mulki kada kuri’a.
“Kwamitin rikon kwarya da tsara zaben APC ya tsaida cewa duk wadanda ke kan mukaman siyasa da aka zaba a matsayin masu kada kuri’a a zaben shugabanni da za ayi a 26/3/2022 ba za su yi zabe ba.
“A dalilin sabanin da ake samu a game da sashe na 84 (12) na dokar zabe na shekarar 2022.’
“Amma duk da haka, masu rike da mukaman za su iya zama ‘yan sa ido.” - APC.
Rahotonni sun ce sashe na 84(10) na wannan doka da majalisar tarayya ta kawo ta hana duk wanda aka ba mukamin siyasa shiga zaben jam’iyya.
Kafin mutum ya iya kada kuri’a a zaben tsaida ‘dan takara, dole sai ya ajiye mukaminsa tukun.
Tirka-tirka kan dokar zaben 2022
Hakan na zuwa ne duk da wani jigo a jam’iyyar Action Alliance party na kasa, Nduka Edede ya shigar da kara a kotu a Umuahia a kan wannan dokar.
Edede yana ganin sashen wannan doka ya ci karo da wasu bangarorin tsarin mulki na kasa, daga ciki akwai 66(1)(f) 107(1)(f)(137(1)(f) da kuma 182(1)(f).
Za a ba Yarbawa mulki?
Alamu na nuna cewa ba dole ba ne mulki ya fada hannun su Asiwaju Bola Tinubu ko Yemi Osinbajo domin ba a tsaida magana a jam’iyyar APC ba.
Akwai masu ganin kafin a kafa APC shekaru 10 da suka wuce, sai da aka yi yarjejeniyar bayan Muhammadu Buhari, shugabanci zai koma ga Yarbawa.
Asali: Legit.ng