Shugabancin APC: Dalilin da yasa muka miƙa wuya ga ɗan takarar da Buhari ke kauna, Gwamna ya fasa kwai

Shugabancin APC: Dalilin da yasa muka miƙa wuya ga ɗan takarar da Buhari ke kauna, Gwamna ya fasa kwai

  • Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya ce girmamawan da gwamnoni ke wa Buhari yasa suka amince da zaɓinsa
  • An kai ruwa rana a jam'iyyar APC tun bayan da shugaban ƙasa Buhari ya nuna wanda yake son ya zama shugaban APC na gaba
  • Gwamnan ya ce samun mutum kamar Buhari a jam'iyyar siyasa ba kasafai ba, shiyasa ko wane mamba ke bin umarninsa

Abuja - Gwamnan jihar Nasarawa kuma shugaban kwamitin Midiya na babban taron APC na ƙasa, Abdullahi Sule, ya yi bayanin abin da yasa gwamnoni suka amince da zaɓin Buhari.

Tribune Online ta rahoto gwamnan na cewa Shugaba Buhari na goyon bayan tsohon gwamnan Nasarawa, Sanata Abdullahi Adamu, ya zama shugaban APC na gaba.

A ranar Asabar 26 ga watan Maris, 2022, APC zata gudanar da babban taronta na ƙasa wanda zata zaɓi shugabanninta.

Kara karanta wannan

Gwamnonin APC: Duk wanda Buhari ya zaba a taron gangamin shi za mu marawa baya

Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule.
Shugabancin APC: Dalilin da yasa muka miƙa wuya ga ɗan takarar da Buhari ke kauna, Gwamna ya fasa kwai Hoto: ripplesnigeria.com
Asali: UGC

Da yake jawabi ga manema labarai game da shirin da kwamitinsa ya yi, Gwamna Sule ya ce masu shakku kan zabin Buhari sun amince ne saboda girmamawan da Buhari ke samu daga masu faɗa a ji.

Ya ce:

"Abin da sauran jam'iyyu suka rasa mu muke da shi, shi ne jagoran siyasa kuma Uba, wanda kowane mamban APC yana matukar ganin girmansa, kuma ba kowa bane illa shugaban kasa Buhari."
"Muna da yaƙinin cewa ba zai taɓa yin abu domin son zuciyarsa ba, ko wani abu daban da zai saɓa wa tsarin jam'iyya. Mutum ne dake sha'awar tabbatar da haɗin kan jam'iyya."
"Wannan shi ne jagoran da muke da shi wanda duk lokacin da yake jawabi kowa tsif yake ya saurara saboda sun san ba zai yi abu don amfanin kan shi ba. Wannan ne rokon sa, kuma tabbas za'a girmama zancensa."

Kara karanta wannan

Taron gangamin APC: Gwamnonin APC sun gana da Shugaba Buhari a Abuja

Zamu yi kokarin shawo kan sauran yan takara - Sule

Gwamnan ya tabbatar wa 'ya'yan jam'iyya cewa zasu yi duk me yuwuwa wajen shawo kan sauran yan takara su janye kudirinsu domin cika sharuddan dokar zaɓe.

"Game da kundin dokar zaɓe, jam'iyyar mu ta na bin doka sau da ƙafa, zamu yi abin da ya dace ba tare da sauka daga kan dokoki ba. Ba zamu bari a yi wani abu da zai saɓa wa doka ba a matsayin jam'iyya mai mulki."

Ya kuma ƙara da ƙarin haske kan shirin kwamitin rikon kwarya na APC ƙarƙashin jagorancin Mala Buni cewa za'a maida wa yan takarar da suka janye don zaman lafiya kuɗaɗen su.

A wani labarin kuma Gwamna a Najeriya ya kori ma'aikata sama da 500 daga aiki, sun fantsama zanga-zanga

Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya amince da korar ma'aikata 513 daga bakin aiki waɗan da ke sashin harkokin wasanni.

Kara karanta wannan

Takara a 2023: Dan takarar shugaban ƙasa ya faɗi gaskiya kan kalaman baiwa ɗan kudu tikitin PDP

A wani kundi mai ɗauke da sanarwan korar ma'aikatan, gwamnan ya ce ya ɗauki wannan matakin domin garambawul ga sashin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262