Sunayen gwamnoni uku da jiga-jigai 34 da zasu yanke wanda PDP zata ba tikitin shugaban ƙasa a 2023

Sunayen gwamnoni uku da jiga-jigai 34 da zasu yanke wanda PDP zata ba tikitin shugaban ƙasa a 2023

  • Jam'iyyar PDP ta fitar da jerin mutum 37 ciki harda gwamnoni uku a kwamitin tsara yankin da ɗan takara a 2023 zai fito
  • Sakataren tsare-tsare na PDP ta ƙasa ya bayyana lokaci da ranar da za'a kaddamar da kwamitin ya fara aiki gadan-gadan
  • Wasu daga cikin masu neman tikitin takara a PDP sun bukaci jam'iyya ta cire maganar yanki-yanki har sai ta samu mulki

Abuja - Jam'iyyar PDP ta zaɓi gwamnoni uku a matsayin mambobin kwamitin mutum 37 da zai yanke hukunci kan yankin da ɗan takarar shugaban ƙasa zai fito.

The Nation ta rahoto cewa gwamnonin sune, gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwai, gwamna Darius Ishaku na jihar Taraba da gwamna Ifeanyi Ugwuanyi na jihar Enugu.

Kara karanta wannan

2023: Ku tsayar dani takarar shugaban kasa zan lallasa kowa a zabe, Gwamnan Arewa ya roki PDP

Jam'iyyar ta ɗauki matakin kafa kwamitin ne a taron majalisar koli (NEC) wanda ya gudana ranar 16 ga watan Maris, 2022.

Tutar jam'iyyar PDP
Gwamnoni uku da wasu jiga-jigai 34 da suka shiga Kwamitin da zai yanke yankin da PDP zata ba takara a 2023 Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Kwamitin zai kuma yi aiki kan yadda za'a raba mukaman shugaban majalisar dattawa, Kakakin majalisar wakilai, Sakataren gwamnati da sauran manyan muƙamai zuwa yankuna shida na Najeriya.

A wata sanarwa da Sakataren tsare-tsare na PDP ta ƙasa, Umar Bature, ya fitar ranar Laraba, ya bayyana sunayen tsofaffin gwamnoni da suka samu shiga kwamitin. Waɗan da duka haɗa da;

Ayo Fayose (Ekiti), Sule Lamido (Jigawa), Ahmed Makarfi (Kaduna), Liyel Imoke (Cross River), Boni Haruna (Adamawa), Ibrahim Dankwabo (Gombe), Ibrahim Shema (Katsina), Ibrahim Idris (Kogi) Attahiru Bafarawa (Sokoto) da kuma Jonah Jang (Filato).

Sauran Mambobin kwamitin da PDP ta kafa

Sauran mambobin da kwamitin ya ƙunsa sun haɗa da, Chief Tom Ikimi (Edo), Mao Ohuabunwa (Abia), Emmanuel Ibokessien (Akwa Ibom), Farfesa A. B. C. Nwosu (Anambra), Sanata Abdul Ningi (Bauchi), Boyelayefa Debekeme (Bayelsa) da kuma Sanusi Daggash (Borno).

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta gamu da babbar matsala, wani jigo tare da dandazon masoya sun koma PDP

Shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilai, Ndudi Elumelu (Delta), Ambasada Franklin Ogbuewu (Ebonyi), Mohammed Abdulrahman (Abuja), Chief Fidelis Izuchukwu (Imo), Ambasada Aminu Wali (Kano), Kabiru Tanimu Turaki, SAN (Kebbi) da Kawu Baraje (Kwara) duk suna daga cikin kwamiti.

Sauran mambobin sune: Chief Olabode George (Legas), Mike Abdul (Nasarawa), Farfesa Jerry Gana (Neja), Daisi Akintan (Ogun), Dakta Omotayo Dairo (Ondo), Farfesa Adewale Oladipo (Osun), da Sanata Hosea Ayoola Agboola (Oyo),

Sai kuma Austin Opara (Ribas), Adamu Maina Waziri (Yobe) da kuma mataimakikn gwamnan Zamfara da aka tsige Barista Mahadi Aliyu Gusau.

Sanarwan ta ƙara da cewa za'a kaddamar da kwamitin domin fara aiki gadan-gadan ranar Alhamis a Sakatariyar PDP ta ƙasa dake Abuja da ƙarfe 11:00 na safe, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

A wani labarin kuma Gwamna Tambuwal ya faɗi hanyar da zasu ɓullo wa Atiku Abubakar game da takarar shugaban kasa a 2023

Gwamnan Sokoto kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a PDP yace zasu zauna da Atiku Abubakar domin yin sulhu game da 2023.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP ta gamu da cikas, ɗan gani kashenin ɗan takarar shugaban kasa ya koma APC

Aminu Waziri Tambuwal ya ce yana da kwarewar da zai kawo wa jam'iyyar PDP nasara, amma ba yana nufin ya fi kowa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262