Yadda zan bi in magance matsalolin kasar nan idan na samu mulki a PDP inji Tambuwal
- Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana manufofin da yake da su idan ya samu shugabancin Najeriya
- Gwamnan Sokoto, Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal ya yi alkawarin magance matsalolin rashin tsaro
- Tambuwal yana cikin masu neman tikitin takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar adawa ta PDP
Sokoto - Mai girma Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto ya yi alkawarin cewa zai yi amfani da fasahar zamani wajen magance matsalar tsaro.
Jaridar The Guardian ta rahoto Gwamna Aminu Waziri Tambuwal yana wannan jawabi a lokacin da ya gana da shugabannin jam’iyyar PDP a Kebbi.
A halin yanzu ana fama da matsalolin rashin tsaro musamman a yankin Arewa maso yammacin Najeriya, inda ‘yan bindiga suka addabi Bayin Allah.
Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana cewa idan ya samu mulki a 2023, zai yi amfani da fasahohin zamani wajen ganin matsalar tsaro ta zama tarihi.
Sai an samar da tsaro tukuna
“Na farko dole mu ga an samar da tsaro, kafin a iya wannan, ya zama dole mu canza tunanin jami’an tsaronmu domin su fahimci halin da ake ciki.”
“Za mu tabbatar an samu isassun kayan aiki na zamani, sannan mu dage wajen kula da walwalar jami’an tsaro, kuma a kara daukar wasu aiki.”
“Kuma mu yi amfani da fasahohi na zamani domin mu yaki ta’addanci da tada zaune tsaye da sauran laifuffuka da ake fama da su a fadin kasar nan.”
“Mun kuma yi niyyar samar da ayyukan yi, ba za mu zauna cikin talauci a Najeriya ba. Idan muka samar da ayyukan yi, za mu magance matsalar tsaro.”
- Aminu Waziri Tambuwal
Harkar noma, ilmi da dogo
Daily Trust ta rahoto gwamnan yana cewa zai maida hankali a harkar noma a Najeriya. A game da batun ilmi, ya ce ya zama dole gwamnati ta tashi tsaye
Bugu da kari, idan shugabancin kasar nan ya shigo hannunsa, zai goyi-bayan ayi wa kundin tsarin mulki kwaskwarima ta yadda jihohi za su kara karfi.
A karshe an ji Aminu Tambuwal yana cewa gwamnatinsa za ta samar da hanyoyin jirgin kasa, inganta wutar lantarki tare da samar da hadin-kan al'umma.
The 2022 Committee
Dazu ne aka ji cewa an yi kwanaki ana wani taron hadin-gambiza da nufin a kawo gyara a 2023. Jiga-jigan PDP da APC sun ajiye sabaninsu, sun halarci zaman.
Shugabannin The 2022 Committee sun yi kira ga ‘yan Najeriya su yi fatali da rade-radin da ake ji, suka ce ba wani ‘Dan siyasa su ke sharewa hanya a zaben ba.
Asali: Legit.ng