2023: Abubuwa 3 da za su kawowa burin Saraki tasgaro na zama Shugaban Najeriya

2023: Abubuwa 3 da za su kawowa burin Saraki tasgaro na zama Shugaban Najeriya

  • Tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya, Abubakar Bukola Saraki zai yi takara a zaben 2023
  • Dr. Abubakar Bukola Saraki ya fito shafinsa na Facebook, ya ce zai nemi kujerar shugaban kasa
  • Amma wani hanzari ba gudu, akwai kalubalen da ke jiran Saraki a kan hanyarsa ta shiga Aso Villa

Abuja - Babu shakka cewa Abubakar Bukola Saraki zai fito neman tikitin takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP a zabe mai zuwa na 2023.

Mun kawo yadda za ta kaya da Bukola Saraki idan ya tsaya zaben shugaban kasa. Jaridar Daily Trust ta fara kawo wadannan cikas da Saraki zai samu.

Arewa maso tsakiya

Bayan mulkin soja, ba a taba samun wani daga yankin Arewa maso tsakiya da ya zama shugaban Najeriya ba. Saraki ya shiga tsakiyar Arewa da Kudu.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Okorocha ya gana da Buhari kan kudirinsa na son zama magajinsa

Kafin Saraki an yi ‘yan siyasa daga yankinsa har da mahaifinsa Olusola Saraki da Iya Abubakar da su J S Tarka da sun nemi shugabanci, ba su dace ba.

Tsarin karba-karba

Wasu su na ganin cewa lokaci ya yi da mulki zai koma kudancin Najeriya tun da Muhammadu Buhari ya yi wa’adi biyu, hakan zai kawowa burinsa cikas.

Ko da an bar 'Yan Arewa su fito da ‘dan takarar shugaban kasa, Saraki wanda ake yi wa jiharsa kallon-kallo zai gamu da babban kalubale a zaben gwani.

Takarar Shugaban Najeriya
Bukola Saraki yana taya Atiku kamfe Hoto: goluwasola
Asali: Facebook

‘Dan kashi a jikinsa

Tsohon gwamnan yana cikin ‘yan siyasar da aka fi bincike a Najeriya. Ana zarginsa da taba Baitul malin jihar Kwara, wanda hakan zai iya bata masa suna a 2023.

CCB ta zargi Saraki da karya wajen bayyana kadarorin da ya mallaka, amma daga baya an wanke shi. EFCC ma ta zarge shi da hannu wajen mutuwar bankin SGBN.

Kara karanta wannan

Da duminsa: IBB ya bayyana goyon bayansa kan takarar shugabancin kasa da Saraki zai fito

Wanene zabin Benuwai?

A jiya ne aka ji Gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom ya sha alwashin cewa za su goyi bayan 'dan takarar shugaban kasa wanda zai tsare al’ummarsu ne a 2023.

Samuel Ortom ya bayyana wannan ne a lokacin da ya hadu da tawagar Atiku Abubakar a garin Makurdi. Ana tunanin a zaben 2023, Atiku ma zai sake fitowa takara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng