Sunayen zababbun shugabannin APC 34 na reshen jihohi da uwar jam'iyya ta san da zamansu
- An rantsar da zababbun shugabannin jam’iyyar APC a kusan duka jihohin Najeriya a ranar Alhamis, 3 ga watan Fubrairu 2022 a birnin tarayya Abuja
- Legit.ng Hausa ta kawo sunayen wadannan shugabanni da uwar jam’iyya ta tabbatar da zabensu. Hakan ya na nufin su ne ainihin shugabannin jihohi
- APC ta samu ta rantsar da shugabanta na jihar Zamfara bayan an dade ana kai ruwa rana a kan yadda za a bullo masu bayan sauya-shekar gwamna
Wadannan shugabanni da aka amince da jagorancinsu su ne:
Dr. Kingsley Ononogbu (Abia)
Ibrahim Bilal (Adamawa)
Augustine Ekanem (Akwa Ibom)
Basil Ejike (Anambra)
Babayo Misau (Bauchi)

Kara karanta wannan
Jiga-jigan da suka yi nasara da wadanda suka sha kasa yayin da APC ta nada shugabanni
Dr. Dennis Otiotio (Bayelsa)
Augustine Agada (Benuwai)
Ali Dalori (Borno)
Alphonsus Eba (K/Riba)
Omeni Sabotie (Delta)
Stanley Emegha (Ebonyi)
Kanal Col David Imuse mai ritaya (Edo)
Omotosho Ayodele (Ekiti)
Ogochukwu Agballah (Enugu)
Nitte Amangal (Gombe)
Dr Macdonald Ebere (Imo)

Source: Facebook
Ragowar sun hada da:
Aminu Gumel (Jigawa)
Air Komodo Emmanuel Jekada mai ritaya (Kaduna)
Muhammed Sani (Katsina)
Abubakar Kana (Kebbi)
Abdullahi Bello (Kogi).
Sunday Fagbemi (Kwara)
Cornelius Ojelabi (Legas)
John Mamman (Nasarawa)
Haliru Jikantoro (Neja)
Yemi Sanusi (Ogun)
Ade Adetimehin (Ondo)
Adegboyega Famodun (Osun)
Isaac Omodewu (Oyo)
Rufus Bature (Filato)
Emeka Bekee (Ribas)
Ibrahim El-Sudi (Taraba)
Muhammed Gadaka (Yobe)
Tukur Danfulani (Zamfara)
Rikicin Kano ya yi kamari
Ku na da labari cewa a halin yanzu da Ahmadu Haruna Danzago da Abdullahi Abbas duk babu wanda uwar jam’iyya ta rantsar a matsayin shugaban APC a Kano.
Ga lokaci ya na neman kurewa jam’iyyar APC, amma har yanzu ba a kammala kokarin sasancin da ake yi wa Gwamna Ganduje da tsagin su Ibrahim Shekarau ba.
Asali: Legit.ng
