Ashe Yari ba ‘Dan APC ba ne – Tsohon ‘Dan Majalisa ya ce tsohon Gwamna bai tare da su

Ashe Yari ba ‘Dan APC ba ne – Tsohon ‘Dan Majalisa ya ce tsohon Gwamna bai tare da su

  • Tsohon ‘dan majalisar Kaura Namoda/Birnin Magaji, Aminu Sani Jaji ya caccaki Alhaji Abdulaziz Yari
  • Hon. Aminu Sani Jaji bai tunanin har yanzu Abdulaziz Yari yana da rajistar zama ‘dan jam’iyyar APC
  • ‘Dan siyasar ya ce idan tsohon gwamnan zai yi wata takara, sai ya sake yin rajista a mazabarsa

Abuja - Tsohon ‘dan majalisar wakilan tarayya, Hon. Aminu Sani Jaji ya yi magana game da rikicin da ake fama da shi a APC a reshen jihar Zamfara.

Jaridar Tribune ta rahoto cewa Aminu Sani Jaji ya na ma zargin cewa tsohon gwamnan jihar Zamfara, Alhaji Abdulaziz Yari ba ‘dan jam’iyyar APC ba ne.

Hon. Jaji wanda ya nemi gwamnan jihar Zamfara a APC a 2019 ya zanta da manema labarai a garin Abuja, inda ya yaba da kokarin Gwamna Bello Matawalle.

Kara karanta wannan

Hotuna: Jam'iyyar APC ta yi babban kamu, fitaccen sanata ya bar PDP ya shigo APC

Tsohon shugaban kwamitin na tsaron cikin gida a majalisar wakilai na kasa ya ce Mai girma Matawalle ya yi kokarin hada-kan 'yan jam’iyyar APC a Zamfara.

Aminu Jaji ya bayyana cewa Gwamna Matawalle ne sabon jagoran jam’iyyar APC a jihar Zamfara, kuma duk da halin rashin tsaro a jihar, za su lashe zabe a 2023.

Ashe Yari ba ‘Dan APC ba ne – Tsohon ‘Dan Majalisa ya ce tsohon Gwamna bai tare da su
Abdulaziz Yari da Hon. Aminu Sani Jaji Hoto: Sowore / Jaji
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yari yana APC?

Daily Post ta ce wannan ya sa aka tunawa Hon. Jaji cewa Yari ya na cikin jam’yyar APC kuma ya na rigima da Gwamna, sai ya nuna an raba jiha da tsohon gwamnan.

Yari yana cikin wadanda suka taka rawar gani tun a jam’iyyar ANPP, har aka shigo APC. Aminu Jaji bai yarda da wannan magana ba, ya ce ba haka abin yake ba.

“Ban san ko Abdulaziz Yari ‘dan jam’iyyan da aka yi wa rajista ba ne. Amma a wuri na, shi ba ‘dan jam’iyyar APC ba ne.”

Kara karanta wannan

2023: Tsohon ‘Dan Majalisar Kano ya hango Tinubu a Aso Villa, ya ba ‘Yan adawa shawara

“Waye ya kafa ANPP? Ta ya aka yi ya kafa APC? Waye shi da zai kafa APC? APC jam’iyya ce, kuma kafin a kafa ta akwai ANPP.”
“Shin Abdulaziz Yari ne ya kafa jam’iyyar ANPP? Hakan ya na nufin gwamnonin ANPP ne suke da jam’iyya.”
“Idan yana neman wani mukami ne a jam’iyya, ya bayyana cewa dole sai ya koma mazabarsa, ya sake yin rajista."

- Aminu Sani Jaji.

Lissafin 2023 a Kudu

Dazu aka ji hankalin Gwamnonin jam’iyyar APC a kudu maso yamma ya rabu a kan zaben 2023 inda aka san cewa Bola Tinubu zai tsaya neman shugabancin Najeriya.

Akwai gwamnoni akalla uku da ake kyautata zaton su na goyon bayan takarar takara Bola Tinubu. Irinsu Gwamnan jihar Ekiti ba ya tare da kowa a halin yanzu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng