Ka nemi kujerar Buhari, mun duba maka – Mataimakin Gwamnan PDP ga Osinbajo

Ka nemi kujerar Buhari, mun duba maka – Mataimakin Gwamnan PDP ga Osinbajo

  • Mataimakin gwamnan jihar Edo ya nuna cewa za su goyi bayan Farfesa Yemi Osinbajo a zaben 2023
  • Philip Shaibu ya bayyana wannan a lokacin da Osinbajo ya je bikin nadin sarautar Clement Agba
  • Shaibu ya ce siyasar Ubangida ta kare a Najeriya, ya ce daukacin matasan Edo za su zabi Osinbajo

Edo - Mai girma mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu ya bayyana Farfesa Yemi Osinbajo a matsayin wanda ya fi dacewa da takara a zaben 2023.

Philip Shaibu ya shaidawa mataimakin shugaban kasar cewa daukacin mutanen jihar Edo su na goyon bayan ya tsaya takarar kujerar shugaban kasa a zabe mai zuwa.

Punch ta ce Mista Philip Shaibu ya bayyana haka ne a wajen bikin nada Clem Agba da aka yi a matsayin Odumhan kasar Auchi a ranar Asabar 29 ga watan Junairu.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Ni da Masari ba mu bacci idanu 2 rufe, Sarkin Katsina ga Osinbajo

Shaibu ya yi jawabi yayin da aka gayyaci Yemi Osinbajo a matsayin bako na musamman a bikin.

“Mai martaba ka san da cewa ka na da jihar Edo, ka na da mu. Duk abin da ke son yi, ka na da mu, kuma ka na tare da Ubangiji.”
“Kuma da yardar Ubangiji na mu ne zai zama shugaban kasar Najeriya a shekarar 2023.” - Philip Shaibu.
Buhari, Osinbajo
Farfesa Yemi Osinbajo da Muhammadu Buhari Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Jaridar Daily Post ta ce Shaibu ya godewa mataimakin shugaban kasar na ajiye duk wasu ayyukan da yake yi, ya halarci nadin sarutar Ministan kasafin kasar.

Mataimakin gwamnan ya ce za su tara matasa da masu jini a jiki domin su karbi ragamar mulki, a cewarsa zanga-zangar EndSARS ta isa al'ummar kasar daukar darasi.

An rahoto Osinbajo yana cewa ta tabbata cewa yanzu matasa za su iya yin abin da ya dace.

Kara karanta wannan

Na sanar da Atiku cewa ya tsufa kuma gajiye ya ke, ba zai iya shugabanci ba, Gwamnan Bauchi

Haka zalika, Shaibu ya ce siyasar iyayen gida ta kare, yanzu zamani ne da za a rika damka mulki ga mutanen da suke son kawo cigaba, masu tunani da za su kawo abin yi.

Zaben shugaban APC

Sanata Sani Musa ya fito da manufarsa da yadda zai bi wajen magance duk wasu rigingimun cikin gida da rikicin Gwamnoni da ke bijirowa jam’iyyar APC mai mulki.

Sani Musa ya ce muddin ya zama Shugaban APC, duk wasu rigingimun jam’iyya sun zama tarihi. Masu fashin baki su na ganin Sanatan yana da goyon Bola Tinubu a APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng