Jiga-jigan siyasan Kudu na neman canza lissafin APC, Tinubu na hada-kai da abokan fada

Jiga-jigan siyasan Kudu na neman canza lissafin APC, Tinubu na hada-kai da abokan fada

  • ‘Yan siyasar Kudu maso yamma za su dunkule domin su samu tikitin takarar shugaban kasa a APC
  • Akwai yiwuwar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da Kayode Fayemi su yi watsi da bambancin ra’ayinsu
  • Su biyun su na da burin neman shugaban kasa a 2023, amma ba za su bari a raba kan yankinsu ba

Abuja - A daidai lokacin da manyan ‘yan siyasa suka fara bayyana niyyarsu na tsayawa takara a zaben 2023, an ji cewa abubuwa na sauya salo a tafiyar APC.

Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar Juma’a, 14 ga watan Junairu, 2022 cewa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da Kayode Fayemi sun yarda su ajiye sabaninsu.

Kafin yanzu, ba a shiri sosai tsakanin babban jigon APC a kudu maso yammacin Najeriya watau Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da gwamnan jihar Ekiti, Dr. Fayemi.

Kara karanta wannan

Hular Tinubu ta yi daraja a kasuwar intanet, 'yan Najeriya sun yi tururuwa domin saye

Abubuwa su na neman canza zani a APC bayan manyan ‘yan siyasar da ake ganin su na shirin takarar shugaban kasa sun yi wani zama a birnin tarayya Abuja.

Rahoton ya ce wannan haduwa na tsohon gwamnan Legas, Bola Tinubu da Gwamna Fayemi ya ba mutane mamaki domin tun 2018 dai ya zamana ba a ga maciji.

Jiga-jigan siyasan APC
Buhari, Tinubu da Fayemi Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tinubu ya samu matsala da Dr. Fayemi bayan ya ajiye kujerar Minista, ya lashe zaben gwamnan Ekiti. Fayemi ya dawo mulki bayan ya gaza yin tazarce a 2014.

Akwai matsala a waje

Wata majiya ta shaida cewa duk da ‘yan siyasar Yarbawan su na da burin fitowa takarar shugaban kasa, sun fahimci su na fuskantar kalubale a wajen gida.

“Saboda haka su ka ga abin da ya fi dacewa shi ne su dinke barakarsu ta cikin gida, su yi magana da murya daya, su gyara alakarsu da sauran bangarori.”

Kara karanta wannan

Burin Tinubu ya gamu da cikas na farko, Shugaban Yarbawan Afenifere ya ki mara masa baya

“Muddin suka yi nasarar yin haka, komai zai iya biyo baya yayin da muke dumfarar zaben 2023.”
“Akwai shirin da wasu suke yi a wajen yankin kudu maso yammacin Najeriya domin su karya su, don haka hadin-kan na su zai taimaka kwarai.” Majiyar.

Babban sakataren yada labarai na gwamnatin Fayemi, Yinka Oyebode yace dama tun can akwai kyakkyawar alaka tsakanin gwamnan da jagoransa, Bola Tinubu.

Tinubu : A kai kasuwa - Afenifere

A makon nan ne shugaban kungiyar Yarbawa na kasa watau Afenifere, Ayo Adebanjo ya yi martani a game da shirin Asiwaju Bola Tinubu na takara a 2023.

Cif Ayo Adebanjo ya bayyana cewa kungiyar Afenifere ba za ta marawa wani ‘dan takara daya baya ba, har sai an canza tsarin mulkin kasar kafin zaben na 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng