Magoya baya sun ba Sanatan APC kwana 90 ya ayyana niyyar takarar Gwamna ko su je kotu
- Wata kungiya mai suna Enyen-Nyen Movement a jihar Delta ta na so Ovie Omo-Agege ya yi takara
- Kungiyar ta na ganin Sanatan ya fi kowane ‘dan takara dacewa da kujerar gwamnan jihar Delta
- A cewar ‘yan kungiyar ta matasa, tun da aka ba Delta jiha a shekarar 1991, babu wani alheri da aka gani
Delta - Kungiyar Enyen-Nyen Movement ta wasu matasa a jihar Delta, ta bukaci Sanata Ovie Omo-Agege ya fito takarar gwamna ko a maka shi a gaban kotu.
Vanguard ta bayyana wannan a wani rahoto da ta fitar a ranar Alhamis, 4 ga watan Junairu, 2022.
Wannan kungiya ta Enyen-Nyen Movement ta cin ma wannan matsaya ne bayan wani taron gaggawa da tayi a tsakiyar makon nan a garin Ughelli, Delta.
Kungiyar matasan ta ce tun da aka kafa jihar Delta a tarihi, har yanzu ba a samu wani cigaba ba, domin shugabannin da aka yi a baya sun gaza tabuka komai.
Tsohon gwamnan Zamfara ya sanar da kudirin takarar shugaban ƙasa a 2023, ya samu gagarumin goyon baya
Ganin haka ne ya sa kungiyar take ganin akwai bukatar mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Omo-Agege ya fito ya shiga takarar gwamna.
Meyasa muke tare da Omo Agege?
"Enyen-Nyen Movement kungiyar matasa ce a Delta da ke neman kwararren ‘dan siyasa wanda zai fitar da jihar daga kangin rashin cigaba da ya karbi mulki.”
“Bayan la’akari da duka ‘yan takarar gwamna a zaben 2023, mun amince mu tallata Ovie Omo-Agege.”
“Sanata Ovie Omo-Agege ya nuna kishin mutanensa yake yi, ya taimakawa mutanen mazabarsa, ya kawo masu ayyuka da suka yi tasiri, kowa ya amfana da shi.”
Wadanda aka yi zaman da su
Wadanda suka sa hannu bayan wannan zama da aka yi su ne: Frank Okeoghene Waive, Kingsley Omokaro, Akpebe Oreva, Godswill da Elimihele Emmanuel.
Ragowar wadanda aka yi zaman da su, su ne: Akpoguma Matthew, Omuaro Prince Urukpe, Diamreyan Nelson, Lugard Oveghawo, da kuma Akpoviri Rita.
Sai Niko Gabriel, Edafe Hitler, Ambrose German, Stanely Omokete, Tega Ibodje, da Felix Godspower.
“Mu na jira.”
“Mu ‘yan wannan kungiya mun gaji da hakuri da Sanata Ovie Omo Agege."
"Daga lokacin da muka rubuta wannan takarda, mun ba shi kwana 90 ya bayyana shirin takara, ko ya amsa karar da za mu kai shi a kotu.” - Kungiyar Enyen-Nyen.
Asali: Legit.ng