Tsohon gwamnan Zamfara ya sanar da kudirin takarar shugaban ƙasa a 2023, ya samu gagarumin goyon baya
- Wata kungiya ta sadaukar da kanta wajen yaɗa manufar takarar shugaban ƙasa na tsohon gwamnan Zamfara, Sani Yerima
- Kungiyar karkashin Yerima Support Organisation (YSO), ta raba wa mambobinta wayoyi da motoci domin fara yakin neman zabe
- Tsohon gwamnan Zamfara, Sanata Sani Yerima, ya sanar da kudirin takararsa tun a watan Yuni, 2021
Zamfara - Wata kungiya masu hidima ga al'umma da ta ƙunshi magoya bayan Sani Yerima, tsohon gwamnan Zamfara, ta fara shirye-shiryen tallata ɗan takararta a 2023.
The Cable ta rahoto cewa wannan na zuwa ne bayan Yerima, jigo a jam'iyyar APC, ya sanar da kudirinsa na neman tikitin takarar shugaban ƙasa a baban zaɓen 2023.
Kungiyar wacce ke karkashin Yerima Support Organisation (YSO), ta raba wa ƴaƴanta wayoyi, motoci da sauran kayayyaki a shirinta na fara yaɗa manufofin tsohon gwamnan.
2023: Ina fuskantar matsin lamba kan cewa in fito takara, in kuma ziyarci Buhari in sanar da shi, Orji Kalu
Da yake jawabi a wurin taro wanda ya gudana a Ibadan, jihar Oyo ranar Laraba, Hadimin Yerima na musamman, Oluyemi Olusina, yace kungiyar ta yanke mara wa Yerima baya a 2023.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Meyasa suka zabi goyan bayan Yerima?
Olusina ya bayyana cewa ƙungiyar ta ɗauki matakin mara wa takarar Yerima baya, duba da nasarorin da ya samu lokacin yana gwamna da kuma Sanata.
Haka nan ya tabbatar da cewa sun sanar da tsohon gwamnan irin aikin da ƙungiyar ta fara, duk da har yanzun yana shawari ne kan kudurin nasa.
The Nation ta rahoto Yace:
"An shirya wannan taron ne domin rantsar da waɗan da suka sa kan su da goyon bayan kudirin takarar Yerima, karkashin YSO, wacce ta kunshi duk wasu dake mara wa tafiyar Yerima baya."
"Muna da akalla mutum miliyan 10 ƙarƙashin wannan kungiya YSO 2023. Wannan babban nasara ce da muka samu cikin shekara ɗaya."
Mutanen da suka shiga tseren takara bayan Yerima
Bayan Yerima, wanda ya sanar da kudirin takararsa tun a watan Yuni, 2021, sauran waɗan da suka shiga tseren sun haɗa da Bola Tinubu, jagoran APC na ƙasa.
Kazalika, gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi, da kuma tsohon shugaban majalisar dattijai, Anyim Pius Anyim, duk sun shiga tseren tikitin takara a 2023.
A wani labarin kuma Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya dira jihar Ogun, ya fara kaddamar da ayyuka
Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya isa jihar Ogun, a wata ziyarar aiki ta kwana ɗaya, da zai kaddamar da wasu muhimman ayyuka da gwamna Dapo Abiodun, ya aiwatar.
Shugaban ƙasan, wanda ya yi shigar Agbada, ya isa Gateway City Gate Monument, tare da gwamna Dapo Abiodun, na jihar, da misalin ƙarfe 11:37 na safiyar Alhamis.
Asali: Legit.ng