An ji Gwamnan PDP ya na yi wa Tambuwal kamfe, yace shi ya dace da Najeriya a yanzu
- Gwamna Ifeanyi Okowa ya kaddamar da wasu ayyuka da Aminu Waziri Tambuwal ya yi a Sokoko
- Da yake jawabi a garin Sokoto, Dr. Ifeanyi Okowa yace Najeriya ta na neman mutum ne irin Tambuwal
- An ji Gwamnan na jihar Delta ya na yabon halin Rt. Aminu Tambuwal, yace ya kawo cigaba a Sokoto
Sokoto - A wani yanayi da ake ganin ya sabawa matsayar gwamnonin kudancin Najeriya, an ji Ifeanyi Okowa, ya na yi wa Aminu Waziri Tambuwal kamfe.
Jaridar This Day ta fitar da rahoto a ranar 3 ga watan Disamba, 2021, inda aka ji gwamnan Delta, Dr. Ifeanyi Okowa, ya na yabon Hon. Aminu Waziri Tambuwal.
Yayin da yake kaddamar da wata cibiyar kula da lafiya ta SOSAMEDIC da gwamnatin Sokoto ta gina, gwamna Okowa ya yabawa takwaransa, Aminu Tambuwal
Gwamnan na jihar Delta ya bayyana tsohon shugaban majalisar wakilai, Tambuwal a matsayin mutumin da kasar Najeriya ta ke bukata a daidai wannan lokaci.
Har ila yau, Ifeanyi Okowa ya yi wa gwamnan na Sokoto addu’a, ubangiji ya daga shi a siyasa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Zuwa na nan (jihar Sokoto), na ga yadda yake mu’amala da mutanensa. Wannan shi ne abin da Najeriya ta ke bukata.”
“Kai mutum ne mai son zaman lafiya, mai kokarin hada-kai. Mun godewa Ubangiji da ya sa ka rike mukamai da yawa.”
“Addu’ar da na ke yi maka shi ne Ubangiji ya daukaka matsayinka.” – Dr. Ifeanyi Okowa.
Vanguard tace jawabin Ifeanyi Okowa ya fito ne ta bakin hadimin gwamnan Sokoto, Mohammed Bello.
Okowa ya yabi Sarkin Musulmi
Har ila yau, a wajen kaddamar da wannan cibiya, Okowa ya yabi Mai alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar, wanda ya ce ya na da kishin kasa.
Okowa ya ji dadin ganin wannan cibiya da gwamnatin Tambuwal ta gina, yace bai yi mamaki ba domin gwamnan ya bunkasa harkar ilmi da kiwon lafiya a Sokoto.
'Dan shekara 28 zai nemi babbar kujera a APC
Abba Ahmad Dangata, wani matashi da ke karatu a jami'a, ya na sha’awar rike mukamin shugaban matasan jam'iyyar APC na kasa a zaben da a za ayi a 2022.
Malam Dangata ya na neman koyi da sa’ansa, wani matashi, Mohammed Kadade Sulaiman wanda ya zama Shugaban matasa na jam'iyyar PDP, ya na shekara 25.
Asali: Legit.ng