2023: Duk ‘Dan shekara 60 ya hakura da neman mulki – CNYF ta ba Atiku, Tinubu jan-kati
- Concerned Northern Youth Forum ba ta goyon bayan dattijo ya karbi shugabancin Najeriya a 2023
- Shugaban kungiyar CNYF, Abdulsalam Moh’d Kazeem, ya bayyana wannan jiya a garin Kaduna
- Kwamred Abdulsalam Kazeem ya na so masu shekara 60 su hakura da takara, su bar wa matasa
Kaduna - Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto cewa an bukaci duk ‘dan siyasar da ya kai shekara 60, ya ajiye maganar neman kujerar shugaban kasa a 2023.
Kungiyar Concerned Northern Youth Forum (CNYF) ta wasu matasan Arewa masu kishin kasa ta bayyana wannan matsaya da ta dauka jiya a garin Kaduna.
Mai Magana da yawun bakin kungiyar, Kwamred Abdulsalam Moh’d Kazeem, ya yi kira ga matasa su yi amfani da damar da suke da ita, su shiga siyasa.
Tun da yanzu an dawo dokar ‘Not too young to run’, Abdulsalam Moh’d Kazeem, yana ganin lokacin ya yi da za a gwabza da matasa wajen neman mulki.
Matsalar kasar nan sai matashi
Da yake jawabi a ranar Litinin, shugaban wannan kungiya ta kasa, Abdulsalam Moh’d Kazeem, ya yi kira ga masu jini a jika da su zo, su kawo gyara a kasar nan.
Shugaban kungiyar matasan Arewan na reshen jihar Kaduna, Nasiru Aliyu ya shaidawa manema labarai cewa Najeriya ta na bukatar rikon matasa ne a yau.
An rahoto Aliyu yace matashi ne zai iya zama dare da rana domin magance matsalolin kasar.
Ya za ayi da Atiku, Tinubu da sauransu?
Ba wannan ne karon farko da aka ji matasan Najeriya sun fito, su na nuna za su goyi bayan ‘dan uwansu matashi a zaben mai zuwa na shekarar 2023 ba.
Idan aka bi ta wadannan matasa, ‘yan siyasa irinsu Atiku Abubakar, Bola Tinubu, Rabiu Musa Kwankwaso ba za su kai labari ba domin duk sun zarce 65.
Daily Trust tace a daidai wannan lokaci wasu ‘ya ‘yan PDP na yankin Arewa maso tsakiya su ka fito su na goyon bayan takarar Abubakar Bukola Saraki.
Shugaban wannan tafiya, Farfesa Iyorwuese Hagher ya bayyana wannan da ya zanta da wasu ‘yan PDP a babbar sakatariyar jam’iyya ta jihar Nasarawa.
Buhari ya dawo daga rakiyar tallafin mai
Kafin ya rike madafan iko, kun ji cewa Muhammadu Buhari ya na cikin wadanda suka yi zanga-zanga saboda za a kara farashin litar fetur daga N65.
Da yake yakin neman zabe, ‘dan adawan a wancan lokaci yace fetur ya yi tsada. Bayan hawansa mulki, Buhari ya dage a kan sai an cire tallafin fetur.
Asali: Legit.ng