Jiga-jigan APC a Kudu sun bayyana abin da zai faru da zarar Tinubu ya zama Shugaban kasa
- Wasu ‘ya ‘yan APC a jihar Ribas su na tare da Asiwaju Bola Tinubu a zaben shugaban kasa na 2023
- ‘Yan tsagin Sanata Magnus Abe sun bayyana cewa alamu sun tabbata cewa Bola Tinubu zai yi mulki
- Wogu Boms da Wilson Ake sun sha alwashin ganin Tinubu ya karbi shugabanci a hannun Buhari
- Boms yace ba kamar halin da ake ciki a yanzu ba, kowa zai shana da zarar Tinubu ya shiga Aso Villa
Port Harcourt, Rivers – Wasu daga cikin kusoshin jam’iyyar APC na reshen jihar Ribas, sun nuna suna tare da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a zaben 2023.
Jaridar PM News tace ‘yan bangaren Magnus Abe a Ribas, suna goyon bayan takarar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ko da bai fito ya bayyana niyyar takara ba.
Jiga-jigan a APC da ke tsagin Sanata Magnus Abe sun bayyanawa Duniya cewa su na so tsohon gwamnan jihar Legas ya zama shugaban kasar Najeriya.
‘ya ‘yan jam’iyyar sun bayyana goyon bayansu ga Bola Tinubu yayin da suke magana a sakatariyar yakin neman zaben Abe da ke garin Fatakwal, jihar Ribas.
Bola Tinubu Vanguard a Fatakwal
Rahoton yace mutanen tsohon Sanatan sun yi jawabi ne a karkashin tafiyar Bola Tinubu Vanguard.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Daya daga cikin jagororin wannan tafiya, Wogu Boms, yace alamu sun tabbata a fili cewa jagoran APC na kasa, Bola Tinubu ne zai karbi shugabanci a 2023.
Abin da zai faru idan Tinubu ya hau mulki
Tsohon kwamishinan shari’ar kuma Darekta Janar na Freedom House ya yi wa al’umma albishir da cewa kowa zai ji dadi idan har gwaninsa ya kai ga mulki.
“Ya kara bayyana a fili cewa Tinubu zai zama shugaban kasa. Idan ya hau mulki, kowa zai shana. Ba kamar wannan ba da mutum daya yake holewa.”
“Mu ne mu ka sa Buhari ya zama shugaban kasa, za mu sa Tinubu ya karbi mulki.” – Boms.
Shi ma Sanata Wilson Ake ya yabi Tinubu a wajen taron, yace a cikin sauran wadanda za su nemi tikitin takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, shi ya fi cancanta.
“Da Tinubu yake yi wa APC aiki, babu wanda ya yi maganar shekarunsa. Yanzu ana cewa ya tsufa, ba za ayi watsi da kwarewarsa don shekarunsa ba.” – Ake.
Za a je kotu a kan aben Anambra
Mun ji za a je kotu a kan zaben Anambra inda wasu lauyoyi suka kai Farfesa Charles Soludo gaban Alkali, su na zarginsa da yi wa INEC karya wajen cike fam.
Alkali yace ranar 30 ga watan Nuwamban 2021 za a zauna domin ya zartar da hukunci. Lauyan zababben ya bukaci Alkali ya yi fatali da wannan kara da aka kawo.
Asali: Legit.ng