Wasu matasan Arewa na goyon-bayan Gwamnan PDP, sun ce shi zai iya gyara Najeriya a 2023

Wasu matasan Arewa na goyon-bayan Gwamnan PDP, sun ce shi zai iya gyara Najeriya a 2023

  • Kungiyar Tambuwal Volunteers tace tsarin karba-karba da ake so a runguma bai yi wani amfani ba
  • Shugaban Tambuwal Volunteers na kasa, Bilal Sidi Abubakar yana yi wa gwamnan Sokoto kamfe
  • Kwamred Bilal Sidi Abubakar yana ganin babu wanda ya dace da rike Najeriya irin Aminu Tambuwal

Abuja - Wata kungiyar matasan Arewa tace tsarin karba-karba da ake kira a runguma a zabe mai zuwa na 2023, ba zai tsinanawa Najeriya komai ba.

Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar Talata, 2 ga watan Nuwamba, 2021, inda aka ji cewa kungiyar Tambuwal Volunteers ta kira taron ‘yan jarida a Abuja.

Shugaban Tambuwal Volunteers, Kwamred Bilal Sidi Abubakar yace mulki ya zagaya Kudu da Arewa, don haka ya dace yanzu a zabi wanda ya dace.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Matasan arewa sun nuna goyon bayansu ga shahararren dan siyasar kudu

Me ya kamata ayi a zaben 2023?

“An yi aiki da karba-karba tun 1999, kuma duk Kudu da Arewa sun fito da shugaban kasa, amma har yanzu ba mu cigaba ba.”
“Muna bukatar wanda ya cancanta ne ya zama shugaban kasa a 2023, domin an bar kasar nan a baya.” - Bilal Sidi Abubakar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kwamred Sidi Abubakar ya shaidawa Daily Trust cewa Tambuwal Volunteers, kungiyar matasa ce da aka kafa domin goyon bayan Aminu Waziri Tambuwal.

Wannan kungiya za ta dage wajen ganin gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya fito takarar neman shugaban kasa a 2023, domin ya gyara Najeriya.

Najeriya a 2023
Aminu Tambuwal yana kamfe a Sokoto Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Najeriya ta na cikin mawuyacin hali - Sidi Abubakar

Shugaban kungiyar yace kasa ta shiga wani mawuyacin hali da ake bukatar shugaba irin Tambuwal.

“Yan bindiga, masu garkuwa da mutane da ‘yan ta’adda sun sa kasarmu a gaba. Ana ta kiran a barka Najeriya ko ta ina.”

Kara karanta wannan

An gano yadda Wike, Tambuwal da Gwamnoni suka raba mukaman PDP a tsakaninsu

“Tattalin arzikin mu ya sukurkuce a gida da waje. Ana fama da yunwa a kasa, kan jama’a ya rabu.” - Bilal Sidi Abubakar.

A jawabinsa, Bilal Sidi Abubakar ya yi kira ga jama’a su gyara kuskuren da aka yi a baya a 2023, yace idan har aka koma gidan jiya, mutane za su kuka da kansu.

Zaben shugabannin PDP

A baya kun ji cewa gwamnoni suka yi abin da suka so a zaben shugabannin PDP, inda har ‘Dan takarar Namadi Sambo ya sha kashi wajen neman mukami a NWC.

Bukola Saraki ya tsira da kujera daya a zaben da aka yi, sannan kuma babu labarin wata kujera da aka ba tsagin tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso a PDP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng