Gwamnatin Buhari za ta sake komawa kotu da Sanatan da ya fito daga gidan yari a 2020
- Gwamnatin tarayya tana so ta sake yin wata shari’a da Orji Uzor Kalu a kotun tarayya
- Hukumar EFCC ta bukaci kotu ta bada dama a maimaita shari’a da tsohon Gwamnan
- EFCC tayi nasarar daure Kalu a gidan yari, daga baya ne kotun koli ta fito da shi a 2020
Abuja - Gwamnatin tarayya ta nemi kotun daukaka kara da ke garin Abuja, ta bada umarnin ayi wa tsohon gwamnan Abia, Orji Uzor Kalu, sabuwar shari’a.
Daily Trust tace gwamnatin Najeriya tana so a koma kotu da Sanata Orji Uzor Kalu a kan zargin satar Naira biliyan 7.1 a lokacin da yake gwamnan jihar Abia.
Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa ta shigar da kara a babban kotun, tana so a rusa hukuncin babban kotun tarayya.
A watan Satumban 2021 ne Alkalin babban kotun tarayya da ke zama a garin Abuja ya dakatar da yunkurin sake gurfanar da Uzor Kalu da kamfaninsa a kotu.
Rahoton yace EFCC tana so kotu ta bada umarnin cewa tsohon gwamnan da kamfanin Slok su gabatar da kansu gaban Alkali domin a iya sauraron shari’arsu.
Rotimi Jacobs ya daukaka kara a kotu
Premium Times tace hukumar ta EFCC ta gabatar da wannan roko ne a takardun da lauyansu, Rotimi Jacobs ya shigar bayan hukuncin Alkali Inyang Ekwo.
Da yake zartar da hukunci a kotun tarayya, Mai shari’a Inyang Ekwo yace sake gurfanar da Kalu da kamfaninsa bayan kotun koli ta wanke shi, ba daidai ba ne.
Kotun tarayyar da ke zama a Abuja ya gamsu da rokon lauyoyin wadanda ake kara. Alkali yace a ajiye batun sake shiga kotu da Sanata Kalu da Jones Udeogu.
Orji Uzor Kalu bai so ya sake shiga kurkuku
Lauyoyin EFCC suna so Kalu wanda yanzu haka shi ne mai tsawatarwa a majalisar dattawa ya koma gidan yari, inda aka taba yanke masa daurin shekaru 12.
Da jin EFCC ta je kotu, Sanatan ya yi wuf ya shigar da kara, yana neman a hana sake gurfanar da shi.
Nyesom Wike ya dura kan Gwamnatin APC
Jiya aka ji Nyesom Wike ya yi wa Gwamnatin Muhammadu Buhari kaca-kaca wajen taron NBA, yace ana yi wa ‘yan adawa cinne, an karbe masu fasfon fita waje.
Gwamnan ya koka da yadda ake fama da matsalar tsaro da tauyewa ‘yan kasa hakkokinsu. Wike yace ana yi wa mutanen sharrin sun zama barazana ta fuskar tsaro.
Asali: Legit.ng