‘Dan shekara 25 ya fito takarar kujerar Shugaban matasa na jam’iyyar PDP na Najeriya
- Prince Muhammad Kadade Suleiman zai nemi shugaban matasa na PDP na kasa
- Santurakin Nasarawan Doya matashin ‘dan siyasa ne mai shekara 25 rak a Duniya
- A karshen watan nan PDP za ta shirya zaben ta na kasa inda Kadade za su gwabza
Kaduna - An samu wani matashi shakaf, Prince Muhammad Kadade Suleiman, da yake neman kujerar shugaban matasa na jam’iyyar PDP na kasa.
A karshen watan Oktoba ne PDP za ta gudanar da zaben shugabanni na kasa. Muhammad Kadade Suleiman ya na sa ran samun nasara a wannan zabe.
Legit.ng Hausa ta samu labari cewa Muhammad Kadade Suleiman mai shekara 25 da haihuwa, ya kudiri niyyar zama shugaban matasan PDP a Najeriya.
A kason da aka yi, Arewa maso yamma za ta dauki kujerar shugaban matasa a jam’iyyar PDP. Kadade ya ci sa’a domin ya fito ne daga jihar Kaduna.
Wanene Muhammad Kadade Sulaiman?
Kadade Sulaiman wanda yake rike da sarautar Santurakin Nasarawan Doya ya na bayyana kansa a matsayin ‘dan siyasar da yake yi da al’ummar kasa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wannan matashi ya karanta ilmin siyasa a jami’ar jihar Kaduna watau KASU tsakanin 2015 da 2019, Kadade ya yi sakandare a makarantar nan ta NTIC.
Kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Facebook, shi jika ne a wurin Sarkin Nasarawan Doya, kuma mahaifinsa ya rike sarautar Danmalikin Zazzau.
Matashin ‘dan kasuwa ne mai neman na kan shi, shi ne yake da kamfanin Dakasu Ventures Nig. LTD.
Abin da ya sa Kadade ya ke neman kujera a PDP
A cewar Abdulhaleem Ishaq Ringim wanda abokin wannan matashi ne, Kadade ya na neman wannan babban mukami ne ba don kurum yana matashi ba.
“Ba mun shiga zabe ba ne saboda shekarunmu, duk da shekaru na da tasiri a nan. Mun shigo takara ne saboda muna da sha’awar kawo cigaba a jam’iyyarmu.” – Kadade Suleiman.
Prince Kadade Suleiman wanda yake adawa da APC, ya taba yunkurin neman gwamnan Kaduna a karkashin jam’iyyar PDP, daga baya ya hakura da yin takarar.
A ranar Litinin aka ji cewa Kungiyar Masoya na Progressive Consolidation Group su na ta kara huro wuta a kan neman takarar Yemi Osinbajo a zaben 2023.
Shugaban PCG, Aliyu Kurfi yace jita-jitar da ake ji cewa Osinbajo ya yafe shiga takara, ba gaskiya ba ne.
Asali: Legit.ng