2023: Ina da yakinin zan lallasa Atiku, Saraki, da sauransu a zaɓe, Ɗan takarar shugaban ƙasa

2023: Ina da yakinin zan lallasa Atiku, Saraki, da sauransu a zaɓe, Ɗan takarar shugaban ƙasa

  • Fitaccen ɗan jarida kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a PDP ya ce yana da tabbacin zai iya lallasa su Atiku, Saraki da sauran su
  • Dele Momodu,ya ce da yana tunanin ba zai iya nasara a zaɓen fidda gwani ba, da ba zai ayyana neman takara ba kwata-kwata
  • A cewarsa, ya gano matsalolin Najeriya, kuma yan Najeriya shi suke kauna saboda bai taɓa shiga harkar gwamnati ba

Ogun - Ɗan takarar shugaban ƙasa ƙarƙashin PDP, Dele Momodu, ya bayyana yaƙininsa na samun tikitin jam'iyya na zaɓen 2023 dake tafe.

Daily Trust ta rahoto cewa Momodu, zai fafata da jiga-jigan PDP da suka haɗa da Atiku Abubakar, Bukola Saraki da gwamna Tambuwal wajen neman tikitin takarar shugaban ƙasa.

Dele Momodu
2023: Ina da yakinin zan lallasa Atiku, Saraki, da sauransu a zaɓe, Ɗan takarar shugaban ƙasa Hoto: dailtrust.com
Asali: UGC

Da yake jawabi ga manema labarai a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, Momodu, ya ce yana da yakinin lallasa sauran yan takara ya lashe tikitin.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamnan PDP a Arewa ya bayyana shirin da yake na gaje kujerar Buhari a 2023

Ɗan takarar shugaban ƙasan ya jaddada cewa shi ne ya dace ya gaji shugaba Buhari saboda, "shi sabo ne fil kuma bai gurɓata ba."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Momodu ya ce:

"Inda na yi tunanin ba zan lashe tikitin ba, ba zan shiga tseren ba sam. Ina da tabbacin na fi saura cancanta kuma na fi sauran kwarewa."
"Ba wani maganar yankin kudu kaɗai, ko daga kudu kake ko arewa, ka samu Dele Momodu, wanda ya zo sabo bai taɓa shiga harkar gwamnati ba. Ni.kaɗai ne mulki bai lalata ni ba."

Matsalar da yan siyasa ke jefa Najeriya

Ɗan jaridan ya kuma ƙara da cewa Najeriya ba ta da matsalar kuɗaɗen shiga, sai dai a akwai kurayen yan siyasa da suke kashe kuɗaɗe ta hanyar wofi.

A cewarsa, mafi yawan yan siyasan dake kan madafun iko suna gudanar da rayuwar da tafi ƙarfin kuɗaɗen shigar su.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Kotu ta tura tsohon kwamishina Ɗan Sarauniya gidan gyaran hali

Daga nan sai ya yi kira da a dakatar da kashe-kashe kuɗin gwamnati cikin gaggawa da nufin maida hankali kan ayyukan cigaba.

A wani labarin na daban kuma Kotu ta tura tsohon kwamishina Ɗan Sarauniya gidan gyaran hali

Kotun dake sauraron shari'ar tsohon kwamishina, Muazu Magaji, ta aike da shi gidan Yari har zuwa lokacin da zata sake zama.

Alƙalin kotun, Mai Shari'a Aminu Gabari, ya umarci a cigaba da tsare Ɗan Sarauniya, kuma a tura likitoci su duba lafiyarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262