Shahararren mawaƙin Najeriya, Wizkid, ya ce bai yarda da addini ba

Shahararren mawaƙin Najeriya, Wizkid, ya ce bai yarda da addini ba

  • Ayodeji Balogun, shahararren mawakin Najeriya da aka fi sani da Wizkida ya bayyana cewa bai yarda da addini ba
  • Balogun ya bayyana hakan ne a cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta a manhajar Snapchat
  • Cikin rubutun da ya wallafa, ya kuma bayyana cewa ba yawan shekaru bane ke nuna mutum na da hankali don ya san wasu masu yawan shekaru amma ba hankali

Shahararren mawakin Najeriya Ayodeji Balogun, wanda aka fi sani da Wizkid ya bayyana cewa shi bai yi imani da addini ba, Daily Trust ta ruwaito.

Balogon ya bayyana hakan ne cikin wata wallafa da ya yi a dandalin sada zumunta ta Snapchat.

Shararren mawaƙin Najeriya, Wizkid, ya ce bai yarda da addini ba
Wizkid: Shararren mawaƙin Najeriya ya ce bai yarda da addini ba. Hoto: Wizkid Dayo
Asali: Depositphotos

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Don ka yi karatu bai zama dole ka samu aikin Gwamnati ba, Buhari ga Matasan Najeriya

Ya ce:

"Bana tashi daga barci da bakin ciki, bana farka wa cikin talauci a rayuwa, cikin koshin lafiya da kyakyawar ruhi kuma bana tashi da kiyayya a zuciya ta.
"Kada ka bata rayuwar ka kan abubuwa masu wucewa. Ka more rayuwa, shekaru ba ya nuna cewa kana da basira, na san mutane masu shekaru sosai amma ba su da hankali kuma ban yi imani da addini ba."

Martanin wasu 'yan Najeriya

phixialvictor:

"WiZkid ya sayar da ruhinsa, na tabbatar da hakan."

_therealtito:

"Ya fada abin da ya fada!"

pinzle_ceo:

"Dukkan abin da ya fada gaskiya ne zalla."

bod_republic:

"Mummy GO za ta yi fushi fa."

dola_official:

"Alakar mutum tsakaninsa da Ubangiji shine ya fi muhimmanci."

Janyandre44:

"Daga cewa Allah ya min albarka, kudi ya zo 'ban yarda da addini ba."

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164