An gano wani faifan bidiyo inda hadimin shugaban ma'aikatan gwamnatin Gombe ke zabgawa kansila masuka kan zargin ya ce zai mari mai gidansa saboda wai an biya shi.
An gano wani faifan bidiyo inda hadimin shugaban ma'aikatan gwamnatin Gombe ke zabgawa kansila masuka kan zargin ya ce zai mari mai gidansa saboda wai an biya shi.
Kotu da ke zamanta a Legas ta ce ta na hurumin sauraron tuhume-tuhumen da hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati ta shigar a kan Emefiele.
An yi wata arangama tsakanin yan ta'adda a jihar Kaduna inda aka hallaka sanannen shugaban 'yan bindiga, Kachalla Dogo Isah a rigimar da ta balle.
Rundunar 'yan sanda ta gwabza da 'yan ta'adda a jihohin Nasarawa, Benue da Bayelsa. An kashe 'yan bindiga a Benue, an ceto mutane a Nasarawa da makamai a Bayelsa
Rahoton Ofishin Mai Binciken Kudi na Kasa ya zargi hukumomin man fetur guda biyu na NUPRC da NMDPRA da rashin yin bayani a kan batan wasu biliyoyin Daloli.
Rundunar 'yan sanda, Amotekun gwamnoni da sauran jami'an tsaro domin dakile 'yan bindiga masu hijira daga Arewa ta Yamma zuwa Kudu bayan sanarwar gwamnan Oyo.
Jami'an tsaron hadin gwiwa da suka hada da 'yan sanda da na rundunar tsaron Sokoto sun samu nasarar dakile wani harin da 'yan bindiga suka kai kan matafiya.
Gwamnatin tarayya ta amince kamfanonin sadarwa su yi ƙarin kudin kiran waya, sako da sayen data amma ba zai kai kaso 100% ba in ji ministan sadarwa, Bosun Tijani.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi martani ga jam'iyyar APC kan shirinta na ganin mulkin Kano ya dawo hannunta a zaben 2027. Ya ce Allah ke ba da mulki.
Kwamoshinan harkokin yawon bude ido, al'adu da fasaha na jihar Kuros Roba, Abubakar Robert Ewa ya mutu a asibitin Kalaba jim kaɗan bayan taron majalisar zartarwa.
Labarai
Samu kari