Gwamnatin Tarayya ta ce tana aiki tare da manyan kamfanonin kafafen sada zumunta domin gano tare da rufe asusun ’yan ta’adda da masu laifuffuka da dama.
Gwamnatin Tarayya ta ce tana aiki tare da manyan kamfanonin kafafen sada zumunta domin gano tare da rufe asusun ’yan ta’adda da masu laifuffuka da dama.
Gwamna Seyi Makinde ya gargadi masu neman ta da rigima bayan an zabi sabon Alaafin na Oyo, Oba Akeem Abimbola Owoade, ta hanyar gaskiya da adalci.
Wasu malaman addinin Musulunci Kudu maso Yammacin Najeriya sun jaddada goyon bayansu ga kudirin dake fasalin harajin da Tinubu ya kai Majalisar tarayya.
Najeriya ta karbi tan 32,000 na shinkafa daga kasar Thailand a yunkurin gwamnati na cika alkawarin da ta dauka na kawo karshen hauhawar farashin abinci.
Majalisar wakilan Najeriya ta jinjinawa sojojin kasar bisa yadda su ka alkinta kasafin kudin 2024 wajen yaki da 'yan ta'addan da su ka hana jama'a sakat.
Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma ya ce cire tallafin man fetur rahama ce ga gwamnatocin jihohi saboda suna samun karin kudi domin gudanar ayyukan ci gaba.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana darajar da nahiyar Afrika ke dashi a duniya. Tinubu ya bayyana matakan da za bi wajen kawo cigaban Afrika a Qatar.
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa jama'ar kasar nan su sa rai da samun faduwar turakun wutar lantarki saboda wasu dalilai da har yanzu ba a magance ba.
Rundunar 'yan sanda ta sanar da kama wani matashi da ya kashe mahaifiyarsa bayan ya mata duka da sanda ya jefa da rijiya tare da hadin kai da abokinsa.
Gwamnan Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya kafa ma'aikatar kiwo domin magance matsala da rikicin manoma da makiyaya da bunkasa tattalin jihar a Itas Gadau.
Labarai
Samu kari