Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a birnin Lokoja na jihar Kogi, ta sauya janye hukuncin da ta bada na tilastawa hukumar INEC yin rajistar jam'iyyar NDC.
Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a birnin Lokoja na jihar Kogi, ta sauya janye hukuncin da ta bada na tilastawa hukumar INEC yin rajistar jam'iyyar NDC.
An samu rahoton cewa mutane da ke aiki da Sunday Igboho domin farautar 'yan bindiga sun hadu da fushin 'yan bindiga. An yi wa mutanen Igboho jina-jina.
Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar hallaka 'yan ta'addan Boko Haram a jihar Borno. Daga cikin miyagun da aka kashe har da wasu kwamandojin kungiyar.
‘Yan bindiga da yawansu ya haura 1,000 sun afkawa garuruwan masarautar Chakfem a Filato, sun kashe mutane 12 ciki har da yara, kuma sun raba jama’a da gidajensu.
Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya gana da jagororin Darikar Tijjaniyya karkashin Sheikh Ibrahim Shehu Dahiru Usman Bauchi. Ya roki a yi wa Tinubu addu'a.
Hukumar ba da agajin gaggawa ta NEMA ta bukaci mutanen da ke jihohin Kebbi, Kwara, Neja da ke kusa da kogin Niger su fara shirin kaura saboda fargabar ambaliya.
Bayan korafe-korafe ya yi yawa kan kisan masallata a jihar Katsina, Gwamnatin ta yi alkawarin cafke wadanda suka kai mummunan hari kan masu ibada.
Wani kamfanin Amurka ya yi hadin gwiwa da jihar Imo wajen kirkiro da shirin tallafawa matasa sama da 3,000 da samu horo kan kasuwancin zamani da jari.
Najeriya ta samu rancen dala miliyan 238 daga Japan domin fadada wutar lantarki, inda za a gina sababbin layuka da tashoshin wuta don rage gibin makamashi.
Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya bukaci 'yan majalisar dokoki su mara wa Gwamna Ahmed Usman Ododo baya, domin ci gaban jihar gaba ɗaya.
Janar Christopher Musa ya ce ana ci gaba da bibiyar masu ɗaukar nauyin ta’addanci a Najeriya, inda hukumomin tsaro da NFIU ke bin sawun kuɗaɗensu.
Labarai
Samu kari