Daya daga cikin manyan 'ya'yan marigayi tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Halima Buhari, ta fito ta yi magana kan wasu halayen mahaifin na ta.
Daya daga cikin manyan 'ya'yan marigayi tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Halima Buhari, ta fito ta yi magana kan wasu halayen mahaifin na ta.
Fusatattun mutane a garin Dansadau sun kai hari ga dan majalisar Zamfara, Kabiru Mikailu, bisa zargin yin watsi da su, yayin ziyarar Gwamna Dauda Lawal zuwa yankin.
Manya a Najeriya ciki har da tsohon hafsan sojoji, Tukur Buratai da tsohon minista, Abubabakar Malami da Godwin Emefiele sun musanta daukar nauyin ta'addanci.
Kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) ta yabawa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu bisa hanzarin da ya yi wajen agaza wa Jamhuriyar Benin tare da dakile juyin mulki.
Rundunar hadin gwiwa ta sojojin Jamhuriyar Benin, sojojin saman Najeriya da dakarun Faransa sun dakile yunkurin juyin mulki a ranar Lahadi da ta gabata.
Majalisar dattawan Najeriya ta amince da bukatar da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar mata, inda yake neman tura dakarun sojoji zuwa Benin.
Sojojin 23 Brigade sun musanta rahotannin cewa sun bude wa fararen hula wuta a jihar Adamawa suna mai cewa ’yan bindiga ne suka harbe mata biyu a tarzomar kabilanci.
Wata kungiya ta yi Allah wadai da shirin Abdullahi Ganduje da mutanensa kan neman kafa sabuwar Hisbah a Kano. Kungiyar ta ce lamarin zai jawo fitina jihar Kano.
Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar ya yi kira da babbar murya ga matasa. Atiki ya bukaci matasa su tashi tsaye ka da su zama 'yan kallo.
Rundunar sojin Najeriya ta karyata cewa ta harbi mata masu zanga zanga a jihar Adamawa. Ya fadi yadda wasu bata gari suka kai wa dakaru hari kuma aka harbe su.
Shugaba Bola Tinubu ya nemi Majalisar Dattawa ta amince a tura dakarun Najeriya Jamhuriyar Benin don taimakawa a zaman lafiya bayan yunƙurin juyin mulki.
Labarai
Samu kari