Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Godswill Akpabio, ya bayyana cewa matsalar rashin tsaron da ake fuskanta na dab da zuwa karshe. Ya bukaci a ci gaba da addua.
Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Godswill Akpabio, ya bayyana cewa matsalar rashin tsaron da ake fuskanta na dab da zuwa karshe. Ya bukaci a ci gaba da addua.
Wani shugaban Tiv ya rubutwa wasika ga Donald Trump na Amurka kan bukatar kai hari Benue da wasu jihohi a Arewa ta Yamma da Arewa maso Gabas bayan harin Sokoto.
Kakakin rundunar yan sanda a jihar Zamfara, Yazid Abubakar, ya musanta rahoton sace masallata 40 inda ya tabbatar da cewa mutane takwas kawai aka dauke a jihar.
Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ya zargi tsohon ministan shari'a Abubakar Malami da ingiza ayyukan ta'addanci, abin da ya sa 'yan kasuwa suka guje wa jihar.
Gwamnatin tarayya ta fitar da sanarwa kan ambaliyar ruwa a wasu jihohi 14 da suka hada da Adamawa, Kebbi Sokoto da Legas. Ambaliya ta riga ta auku a Adamawa.
Gwamnatin tarayya ta kawo sababbin shirye shirye domin bunkasa noma da samar da abinci. Mutane miliyan 21 ne za su samu ayyuka karkashin shirin a Najeriya.
Sheikh Isa Ali Pantami ya tura sakon ta'aziyya ga iyalai da al'ummar Musulunci kan babban rashin malamin addini, Sheikh Ahmad Aladesawe da ya rasu a jiya.
Izala ta Najeriya ta yi rashin daraktan agaji na Katsina, Alhaji Abdullahi Bakori, wanda Sheikh Bala Lau, ya bayyana a matsayin mutum mai riƙon amana.
Yayin da ake mukabala tsakanin mawakan yabon Annabi SAW, Hukumar tace fina-finai ta Kano ta hana duk wani muhawara tsakanin mawakan a jihar saboda rikice-rikice.
Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta sha alwashin dakile talauci gaba daya a fadin Najeriya inda ta ce za ta bi duk hanyar da ta dace domin kawo sauyi a kasa.
Hukumar NiMet, ta fitar da hasashen ruwan sama da zai sauka a ranar Laraba, 17 ga Satumba, 2025, inda ta ce jihohi 13 na Arewa za su samu ruwan daga safe zuwa dare.
Labarai
Samu kari