Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya ce shirin NELFUND ya taimaka wajen rage wa yaran talakawa matsalar kuɗin karatu a manyan makarantu.
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya ce shirin NELFUND ya taimaka wajen rage wa yaran talakawa matsalar kuɗin karatu a manyan makarantu.
Huhu John Gwamna ya bayyana cewa Musulmai ne suka taimaka masa wajen gina aikinsa, yana mai cewa bai taɓa fuskantar wariyar addini a gwamnatin El-Rufai ba.
Gwamna Dauda Lawal ya yi jimamin rasuwar Sarkin Zamfaran Zurmi, Alhaji Bello Sulaiman, wanda ya rasu a asibitin Federal Medical Centre da ke Gusau.
JNI reshen Plateau ta musanta cewa an kafa Hisbah a Jos North, tana mai cewa babu wata ƙungiyar Musulmi da ta sanar da shirin kafa hukumar a yankin.
Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da shirin “Hire from Nigeria” domin hada kwararrun ’yan Najeriya da masu daukar ma’aikata daga kasashen ketare cikin sauki.
Wani SAN a tawagar lauyoyin Tinubu, Wole Afolabi, ya ce da akwai hujjar alakar Shugaba Bola Tinubu da safarar miyagun kwayoyi, da Amurka ta kama ko gurfanar da shi.
Hukumar EFCC ta ce ta kori ma’aikata sama da 40 cikin shekaru biyu da rabi saboda zargin cin hanci da rashawa, yayin da wasu ke fuskantar shari’a.
An samu Duane “Keffe D” Davis da laifin shirya kisan mawaki Tupac Shakur, bayan kusan shekaru 30 ana binciken kisan fitaccen mawakin rap a Amurka.
Hedkwatar tsaron Najeriya ta tabbatar da ceto yan bautar kasa 10 daga cikin 15 da yan bindiga suka yi garkuwa da su bayan sun fito sansanin NYSC.
’Yan bindiga sun kai hari Kano karo na uku a jere, inda suka kashe mutum tare da yin garkuwa da shugaban APC na yankin Rogo, Alhaji Audu Fanka Salisu Yahaya.
Shugaban Kasa Bola Tinubu ya tafi hutu zuwa Turai har na tsawon makonni 3, amma fada ta ce zai ci gaba da kula da harkokin kasar a kullum har ya dawo gida Najeriya.
Labarai
Samu kari