Rahotanni sun nuna cewa an kama wata matar sure, Bilkisu Sani da ke yankin karamar hukumar Rogo ta jihar Kano kan zargin kashe mijinta, Hafizu Gausu.
Rahotanni sun nuna cewa an kama wata matar sure, Bilkisu Sani da ke yankin karamar hukumar Rogo ta jihar Kano kan zargin kashe mijinta, Hafizu Gausu.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike na gaskiya kan mutuwar mutanen da ake zargi da haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba a Neja.
Ministan yada labarai Mohammed Idris ya ce Shugaba Tinubu na shirin inganta walwalar ma’aikatan bangaren yada labarai domin kara bunkasa ayyukan gwamnati.
Jam'iyyar adawa ta PRP ta nuna adawarta karara da yunkurin gwamnatin tarayya na kafa rundunar 'yan sandan jihohi duk da amincewar Majalisar dokoki ta kasa
Shugaban ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Femi Gbajabiamila, ya ce gwamnatin tarayya na shirin sake duba mafi ƙarancin albashin N70,000 saboda tsadar rayuwa.
'Yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci a jihar Katsina. 'Yan bindigan sun hallaka mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba.
Gwamnan jihar Sakkwato, Ahmed Aliyu ya bayyana cewa 80% na matsalar tsaron da ake fama da ita tana da alaka da shan miyagun kwayoyi mussmman a wurin matasa.
Iyalan marigayi fitaccen jarumin Nollywood, Mr Ibu, sun roki ‘yan Najeriya su taimaka musu saboda matsalar kudin makaranta, haya da sauran bukatun rayuwa.
Sojin Najeriya sun gargadi jama’a game da bullar wasu 'yan damfara da ke amfani da bikin NADCEL 2026 wajen neman tallafi da damfarar kudi da sunan rundunar.
Gwamnatin jihar Kebbi ta nuna damuwa kan bullar wata sabuwar kungiyar 'yan ta'adda. Ta bayyana cewa mambobin kungiyar suna gudanar da ayyukansu a jihar.
Rundunar ‘yan sanda ta fara bincike kan bidiyon da ya nuna wani jami’inta yana shan abin da ake zargin giya ce da neman kudi yayin aikin bincike a kan hanya.
Labarai
Samu kari