Ga Dama Ta Samu: WikkiTimes Ta Kaddamar da Shirin 'Femi Falana Legal Defenders'
WikkiTimes, ta hanyar gidauniyarta ta bunƙasa kafafen yaɗa labarai, wato WikkiTimes Media, ta sanar da ƙaddamar da shirin bada horo da tallafi na Femi Falana Legal Defenders (FFLDF).
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Wannan wani sabon shiri ne da aka kaddamar don ƙarfafa kariya ta shari'a ga ƴan jarida, masu fafutukar sa-ido, da masu bincike kan al'amuran yau da kullum waɗanda ke fuskantar barazanar shari'a a Najeriya.

Source: UGC
An kaddamar da shirin Femi Falana Legal Defenders
A karkashin wannan tallafi, shirin zai tunkari dabarun shari'a na tsoratarwa (SLAPP), tuhumar aikata laifuffuka a yanar gizo, da sauran matakan shari'a da ake amfani da su wajen tsoratar da ƴan jarida da dakatar da rahotannin neman gaskiya—wani yanayi da aka fi sani da "amfani da tsarin shari'a a matsayin makami."
Mawallafin WikkiTimes, Haruna Mohammed Salisu, ya bayyana cewa shirin zai horar tare da tallafa wa matasan lauyoyi guda 25 domin gina ƙwarewar shari'a da ake buƙata wajen kare ƴancin ƴan jarida, haƙƙin ɗan adam, da haƙƙin jama'a na sanin gaskiya.
Haruna Salisu ya lura cewa a faɗin Najeriya, ƴan jarida dake bincikar cin hanci da rashawa, laifuffukan muhalli, da gazawar shugabanci, na ƙara fuskantar shari'o'in ɓatanci da tuhume-tuhume a yanar gizo.
Ya bayyana cewa sau da yawa ana daukar waɗannan matakan ba don neman adalci ba, a'a, sai don zama hanyar ƙarar da albarkatun ƴan jarida, jinkirta bincike, da kuma sanyaya gwiwar bayar da rahotannin neman gaskiya.
Ya bayyana cewa an ƙirƙiri FFLDF ne domin taimakawa wajen cike wannan giɓi ta hanyar gina hanyar sadarwa ta lauyoyi waɗanda ke da kayan aikin kare ƴan jarida da masu fafutuka waɗanda ke fuskantar matsin lamba na shari'a saboda ayyukansu.
Dalilin sanya wa shirin sunan Femi Falana
Ya ƙara da cewa jami'ar North-Eastern dake Gombe, da ofisoshin lauyoyi na SG Idrees and Co. Chambers, da kuma Forthright Chambers sune abokan haɗin gwiwa na ilimi da shari'a a wannan shirin.
An sanya wa shirin sunan Femi Falana, SAN, ɗaya daga cikin fitattun lauyoyin kare haƙƙin ɗan adam a Najeriya, a matsayin karramawa ga jajircewarsa na shekaru da dama wajen shari'o'in kare haƙƙin jama'a da ƴancin ƴan jarida.
A tsawon shekaru, an san Mista Falana da ƙalubalantar yadda ake amfani da dokoki ta baibai wajen dakatar da 'yan adawa, da kuma kuntata lauyoyi masu kishin kare haƙƙin ɗan adam.
Matakan shirin Femi Falana Legal Defenders
Shirin zai gudana ne na tsawon watanni 12 a matakai guda biyu
Mataki na farko zai ƙunshi watanni uku na horo mai tsanani ta yanar gizo, inda za a sada zaɓaɓɓun lauyoyin ga muhimman tsare-tsaren shari'a da kayan aikin da ake buƙata wajen kare ƴan jarida da masu fafutuka dake fuskantar barazana.
Wannan horo zai shafi dokokin kafafen yaɗa labarai, haƙƙin tsarin mulki, ƴancin faɗar albarkacin baki a intanet, da kuma yadda ake amfani da dokar Cybercrimes Act a shari'o'in da suka shafi ƴan jarida.
Haka kuma, mahalarta za su yi nazarin amfani da kayan aikin binciken shari'a na zamani da fasahohin dake taimakawa wajen tattara hujjoji da kuma dabarun kare shari'a a matakai masu sarƙaƙiya.
Mataki na biyu na wannan shiri zai ƙunshi watanni tara na aiki a aikace a ofisoshin lauyoyi da ƙungiyoyin bayar da agajin shari'a a faɗin Najeriya.

Kara karanta wannan
Bakin hayaki ya turnuke Tehran, Amurka ta yi wa Iran mummunar barna a karon farko
A wannan lokacin, za su taimaka wa manyan lauyoyi dake gudanar da shari'o'in ƴan jarida, tare da bayar da gudunmawa wajen binciken shari'a da shirya dabarun kariya ga aikin jarida mai zaman kansa.
Lauyoyin za su kuma haɗa kai wajen ƙirƙirar taskar bayanan shari'a da kuma wani tsari mai suna SLAPP Defence Cheat Sheet don lauyoyin Najeriya. Wannan tsari zai zama kundi wajen mayar da martani ga shari'o'in tsoratarwa (SLAPP) kuma zai kasance a buɗe ga kowa bayan kammala shirin.
Yadda WikkiTimes ke tallafawa aikin jarida
WikkiTimes ta bayyana cewa wannan shiri wani ɓangare ne na babban ƙudurinta na ƙarfafa tsarin dake tallafawa aikin jarida na bincike, musamman yayin da ƴan jarida ke ƙara fuskantar haɗarin shari'a.
Masu shirya taron sun lura cewa kare ƴancin ƴan jarida na buƙatar maya da ƴan jarida jarumai, da samar da lauyoyi da suka shirya ƙalubalantar tsoratarwa da kiyaye haƙƙin tsarin mulki.
Ta hanyar shirin FFLDF, WikkiTimes na fatan taimakawa wajen gina sabon ƙarni na lauyoyi masu iya samar da kariya ta shari'a ga ƴan jarida da masu fafutuka a faɗin Najeriya.
Wannan shiri a buɗe yake ga matasan lauyoyi ƴan Najeriya masu sha'awar kare haƙƙin ɗan adam da ƴancin faɗar albarkacin baki, musamman waɗanda ke son amfani da ilimin shari'a wajen kare dimokuradiyya.
Masu sha'awa za su iya neman shiga shirin ta wannan adireshin. Don tambayoyi, za a iya tuntuɓar ƙungiyar ta kamalibrahim@wikkitimes.com ko naganye@wikkitimes.com yanzu.
Asali: Legit.ng

