Hanya Mafi Sauki Ta Karbar USD a Najeriya: Muna Gabatar da Bankin AfriChange na Intanet

Hanya Mafi Sauki Ta Karbar USD a Najeriya: Muna Gabatar da Bankin AfriChange na Intanet

Tsawon shekaru, masu aiki a yanar gizo, kananu da matsakaitan ‘yan kasuwa da ma wasu al’ummar Najeriya, musamman daga Arewa, suna fama da matsala guda daya: Ta ya za ka karbi USD daga Amurka cikin sauri, cikin aminci ba tare da kudinka sun makale ko an zabtare maka su ba?

Bankunan da muka saba amfani da su kan gaza karbar kudadenmu a kan lokaci, sannan suna da tsadar caji, kafin ka iya mallakar asusun karbar USD daga kasar waje sai ka sha wahala. Idan ka ce ka bi bayan fage, to za ka iya haduwa da macuta, su damfare ka.

AfriChange ya zo don canja wannan labari.

Yanzu da aka samar da Africhange, za ka iya daga darajar kasuwancinka zuwa kasashen waje, ka samu abokan hulda da za su rika tura maka kudi cikin sauki.

AfriChange, wata amintacciyar manjahar hada-hadar kudade ce, da take da rajista da dukkan hukumomi a Canada, U.K., U.S., Nigeria, Australia, da sauransu, kuma an samar da kamfanin don kawo karshen wahalar da ‘yan Najeriya ke yi wajen karbar USD daga kasashen waje.

Muna gabatar da bankin AfriChange na yanar gizo

Muna gabatar maku da bankin AfriChange na yanar gizo
Muna gabatar maku da bankin AfriChange na yanar gizo
Source: Facebook

Asusun bankin AfriChange na yanar gizo ya na ba mutane da ‘yan kasuwa a Najeriya damar karbar USD kai tsaye daga bankunan Amurka, ta tsarin ACH da Fedwire.

Hakan na nufin cewa, kamfanoni, abokan kasuwanci, ma’aikata da iyalai da ke zaune a Amurka na iya tura kudinsu gareka kai tsaye, kamar yadda za su iya turawa masu asusun banki a Amurka.

A karkashin wannan tsari:

  • Babu wani shamaki a tsakaninku
  • Babu wata tangardar sadarwa
  • Babu wata wahala ko dawurwura

Kawai, za a tura maka kudi yanzu, ka karbe su yanzu, kuma ka cire su yanzu.

Me ya bambanta AfriChange da sauran?

Manufar samar da AfriChange is ne tabbatar da cewa ‘yan hijira da ke a fadin duniya sun samu hanya mai sauki, mai aminci, mai rahusa ta tura kudi zuwa gida. Burin kamfanin shi ne amfani da sababbin fasahohi da blockchain wajen tura kudi zuwa Afrika cikin sauki ba tare da caji mai yawa ba.

A sani cewa AfriChange ya samu sahalewar hukumomi, kuma yana da rajista da FINTRAC a Canada a matsayin kamfanin hada-hadar kudi ( da lambar rajista M19773759), kuma yana da lasisi a Québec karkashin Revenu Québec (da lambar lasisi 12705).

Yayin da sauran kamfanoni ke ikirarin suna ba da taimako kan hada-hadar kudi ta kasa da kasa, shi AfriChange ya sha bamban da su ta manyan hanyoyi biyar:

1. Ba a biyan ko sisi wajen zuba kudi — Kana da iko kan dukkan kudinka da ka sanya

  • Ba za a caje ka sisin kobo idan ka karbi USD ta asusun AfriChange dinka ba.
  • Ba za ka biya wani kudi don za ka ajiye kudi a asusun ba.

Da wannan kawai, AfriChange ya shiga gaban dukkan sauran bankunan da aka saba da su, da ma wasu da ke hada-hadar kudi na kasa da kasa.

2. Farashin musayar USD-Naira mai kyau

Idan lokacin sauya dala zuwa Naira ya yi, AfriChange na ba da damar yin musayar kudin a farashi mai kyau, wanda ke sa abokan hulda su amfana sosai da duk mu’amalar kudi da suka yi, wanda ke da tasiri ga masu aiki a intanet, masu shigo da kaya da masu karbar kudi daga Amurka.

3. An gina shi kan sauri, tsaro da bin ka’ida

AfriChange ya na aiki ne bisa sahalewar hukumomi da kuma kiyaye ka’idojin kasuwannin da take da lasisi da su. Wannan kamfani na amfani da fasahohin hada-hada masu karfi da tsaro don kare dukiyar abokan hulda.

Wannan na nufin cewa kudin mutum na shiga da fita ta tsarin hada-hadar kudi da aka amince da ita a Amurka, ba wai ta barauniyar hanya ba.

4. Kamfanin da aka samar don ‘yan Afrika

An samar da AfriChange da kuduri daya: saukakawa ‘yan Afrika hada-hadar kudi a farashi mai rahusa kuma a yanayi mai tsaro.

Mallakar asusun bankin yanar gizo na AfriChange zai taimakawa ‘yan Najeriya amfana da duk wani romon tattalin arziki na duniya ba tare da shamaki ba.

5. Garabasa ga sababbin abokan hulda

Domin abokan hulda su ji dadin mu’amala da AfriChange tun a farkon farawa, kamfanin ya samar da garabasa ta yadda sabon kwastoma zai samu rangwamen ₦10 a kan duk musayar kudi da ya yi daga Naira-zuwa-GBP, Naira-zuwa-USD, da Naira-zuwa-CAD.

Wannan na nufin cewa daga sa’ilin da ka sanya kudi a asusunka kuma ka yi hada-hadar kudi, daga lokacin za ka fara adana wasu ‘yan kudade; ba ka bukatar kalmomin sirri, ko wasu sharuda masu tsauri.

Ana iya ganin kudin kamar kadan, amma kuma a hankali za su bunkasa kudin da mutum yake hada hada da su aAfrichange, tare da samun sauki a karba da tura kudade.

Amfanin Asusun Bankin Intanet Ga Arewacin Najeriya

Arewacin Najeriya shiyya ce da ke samun ci gaba kamar wutar jeji ta fuskar masu aiki a intanet, masu kasuwancin kudin intanet, da masu kasuwanci na kasa-da-kasa.

Amma duk da wannan ci gaban, mutane daga manyan birane kamar Kano, Kaduna, Jos, Bauchi da Maiduguri na shan wayar turawa ko karbar kudi daga waje:

Suna shan wahala ta fuskoki kamar haka:

● Karbar kudi daga abokin huldarsu da ke Amurka

● Sauya kudi a farashi mai kyau

● Karbar kudi daga kasashen ketare na hada hadar kayayyaki

● Karbar tallafin kudi daga ‘yan uwa da ke zaune a kasar waje

Asusun bankin AfriChange na yanar gizo ya warware wadannan matsalolin, ya samar da fasahar da za ta sharewa ‘yan Arewa hawaye ta fuskar karbar kudi daga kasashen waje.

Yadda za ka bude asusun AfriChange

Yin rajista domin bude asusun AfriChange na da saukin gaske:

Ga gamagarin mutane

1. A sauke manhajar AfriChange a wayar salula daga shafin africhange.com

2. A kirkiri sabon asusu

3. A kammala dukkan matakan tantancewa

4. A kammala bude asusun yanar gizo domin fara karbar kudi daga waje nan take

Ga kamfanoni

1. A ziyarci shafin business.africhange.com

2. A yi rajistar asusun kamfani

3. A kammala dukkan tantancewar kamfani

4. A samu asusun USD na kamfani da zai ba da damar karbar kudi daga waje nan take

Da zarar an kammala rajista da tantncewa, abokan hulda za su iya fara amfani da asusun AfriChange domin karbar USD nan take.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com