Najeriya Ta Fara Lalubo Hanyoyin Bunkasa Tattalin Arziki Bayan Man Fetur

Najeriya Ta Fara Lalubo Hanyoyin Bunkasa Tattalin Arziki Bayan Man Fetur

Masana a wajen wani taron da bankin First City Monument Bank (FCMB) ya shirya sun yi bayanin cewa ya kamata Najeriya ta sauya akalar tattalin arziƙinta daga dogaro kan albarkatun man fetur

Buƙatar samo wasu sababbin hanyoyin bunƙasa fitar da kayayyakin da ba man fetur ba zuwa ƙasashen waje, shi ne abinda tattaunawar ta fi mayar da hankali a kai.

Bankin FCMB ya yi taro
Manajan Daraktan bankin First City Monument Bank (FCMB), Yemisi Edun
Asali: Twitter

Masu ruwa da tsaki sun nuna irin damarmarki da ke a fannin sarrafa kayan noma, masana'antu da ma'adanai.

Manajan Daraktan bankin FCMB, Yemisi Edun, ta jaddada muhimmancin haɗin gwiwar da ake buƙata domin cimma wannan sauyin.

"Ta hanyar yin aiki hannu da hannu domin samar da ingantaccen yanayin aiki, samar da abubuwan da ake buƙata domin fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen waje da samun isassun kuɗaden da ake buƙata, za mu samar da hanyar yin nasarar ɓangaren fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen waje na Najeriya" Edun ta bayyana hakan inda ta yi nuni da irin rawar da bankin ke takawa a fannin.

Babban mai jawabi a wajen taron, shugabar hukumar bunƙasa fitar da kayayyaki ta Najeriya (NEPC), Nonye Ayeni, ta nuna muhimmancin masu fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen waje su ƙara haɓɓaka kayayyakin da suke samarwa ta yadda za su yi gogayya a sauran ƙasashen duniya.

Ta yi nuni da shirin hukumar na "Export 35 Refined" wanda ya bunƙasa samar da kuɗaɗen shiga ta hanyar ba da taimako ga manyan kayayyakin noma.

Jami'an gwamnati da suka haɗa da shugaban hukumar Kwastam, Adewale Adeniyi, sun yi bayani kan hanyoyin da ake buƙata domin bunƙasa kasuwancin fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen waje da suka haɗa da samar da wuri ɗaya na bincikar kayayyakin da za a fitar da mayar da ayyukan tantancewa bisa kan na'ura.

Manajan Darakta na bankin shigowa da fitar da kayayyaki na Najeriya (NEXIM) Abubakar Bello, ya bayyana shirye-shiryen kawar da matsalar rashin kuɗi da bunƙasa hada-hadar kasuwanci.

Bankin FCMB, wanda ke kan gaba wajen samar da abubuwan da ake buƙata wajen fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen waje, ya sake jaddada ƙudirinsa na tallafawa harkokin kasuwanci domin su shiga kasuwannin duniya.

Ta hanyar mayar da hankali wajen ba da taimakon da ya dace, bankin yana samar da abubuwa irin su kuɗaɗe, shawarwari da bayanai kan yanayin kasuwanni.

Taron ya haska Najeriya a matsayin wacce ta shirya yin na'am da sabon yanayin tattalin arziƙi. Ƙasar za ta iya samar da hanyoyin bunƙasa tattalin arziƙinta ta hanyar yin amfani da tarin albarkatun da take da su da bunƙasa fannin da ba man fetur ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Legit.ng Branded Content avatar

Legit.ng Branded Content (marketing page) This account is used for publishing branded/sponsored content. For any enquiries please email: ads@corp.legit.ng or call: +234 810 304 48 99