Saura Kwana 4 Zabe, Gwamna Buni Ya Dage Tsohuwar Dokar Hana Hawa Babura a Jihar Yobe
- Gwamnatin Yobe ta dage takunkumin da aka sanya kan amfani da babura a wasu kananan hukumomi bakwai na jihar
- Bayan dage haramcin, gwamnatin jihar ta ce ba za a yi achaba ba kuma mutum daya aka yarda ya hau kowani babur daya
- Tun a gwamnatin Ibrahim Gaidam aka sanya wannan takunkumi a kananan hukumomi 17 amma Buni ya sauke na 10 suka rage 7
Yobe - Gwamna Mai-Mala Buni na jihar Yobe ya dage haramci kan amfani da babura a kananan hukumomi bakwai na jihar.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun mai ba Buni shawara kan harkokin tsaro, Birgediya Janar Dahiru Abdulsalam mai ritaya, Daily Trust ta rahoto.

Source: UGC
Jaridar Independent ta nakalto sanarwar na cewa:
"Saboda haka an dage haramci kan babura a Bursari, Damaturu, Geidam, Gujba, Gulani, Tarmuwa daYunusari daga ranar 6 ga watan Maris.

Kara karanta wannan
Daga karshe: Kotu ba da belin dan majalisar Kano Doguwa, an ba shi sharadi kan zaben gwamnoni
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"An dage haramcin ne saboda yanayi, masu babura za su dunga aiki tsakanin 6:00 na safe zuwa 6:00 na yamma a kullun.
"Ba za a dunga yin achaba da babura ba. Ba za a dunga daukar fasinjoji a babura ba.
"Mutum daya kacal aka yarda ya hau babur ba tare da wani mutum a kai ba.
"Ya zamana mai tuka babur din na da cikakken rijista, lasisi da takardun dukkanin babura a kananan hukumomin da abun ya shafa.
"Gwamnatin jihar ta kuma yi umurnin cewa masu babura su dunga aiki a tsakanin kananan hukumominsu kawai.
"Ba za a yi zarya tsakannin kananan hukumomi ba. Duk wanda aka samu ya karya dokar za a yanke masa hukuncin da ya dace.
"An bukaci dukkanin hukumomin tsaro da su lura sannan su tabbatar da ganin an bi doka yadda ya dace."
An sanya dokar hana babura a Yobe shekaru 11 da suka shige

Kara karanta wannan
Saura kwana 4 zabe, kotu ya fadi wanda ya amince ya yi takarar gwamnan Zamfara a PDP
Ku tuna cewa a watan Janairun 2012, gwamnan jihar Yobe na wancan lokacin, Ibrahim Gaidam ya haramta achaba da nufin hana jama'a amfani da shi wajen haddasa rashin tsaro musamman a lokacin rikicin Boko Haram a jihar.
Sai dai kuma Gwamna mai ci, Mai Mala Buni ya dage haramcin a kananan hukumoni 10 cikin 17 na jihar a watan Janairun 2022.
A wani labari na daban, mun ji cewa tsagerun yan bindiga sun farmaki hedkwatar karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara inda suka kashe DPO dfa wasu jami'an tsaro biyu.
Asali: Legit.ng