Mai Ciki Haihuwa Ko Yau Ko Gobe Ta Mutu Sakamakon Faɗa Akan ₦350 a Bayelsa.

Mai Ciki Haihuwa Ko Yau Ko Gobe Ta Mutu Sakamakon Faɗa Akan ₦350 a Bayelsa.

  • Matar tayi rigima da cacar baki ne da wata mata data fita shekaru a duniya.
  • Cacar bakin takai su da faɗa, inda aka Samu Ƙaramar Aka Mata Wata Mahangurɓa a Hanci, Take Jini Yayanke
  • Daga Baya an Kaita Asibiti Inda Tace Ga Garin Ku Nan, Matasa Sunyi Ƙone-Ƙone.

Bayelsa - A lokuta da dama abubuwa na faruwa da suke da sarƙaƙiya ga duk wanda yaji.

Ko a garin kaɓa-kaɓa idan akace mutum zai mutu akan kuɗi, sai anyi mamaki ballanta ace har an rasa rai akan ₦350.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Hakan ne ya faru da wata mata mai suna Uwargida Akumere Aregbare, bayan wata mata mai suna Eniekeduo Atabala mai shekaru 38 ta taƙarƙare ta naushe ta yayin da suke gudanar da musu da cacar baki akan wasu ƴan canji da basu wuce ₦350 ba da take bi.

Kara karanta wannan

Yadda Tururuwar Mutane Sukayi Farin Dango A Kano Domin Tarbar Kwankwaso

Ita dai mamaciyar, ta kasance yar asalin yankin Amassoma dake kudancin ƙaramar hukumar Ijaw ta jihar Bayelsa ne.

pregnantwoman
Mai Ciki Haihuwa Ko Yau Ko Gobe Ta Mutu Sakamakon Faɗa Akan ₦350 a Bayelsa. Hoto: sunnewsonline.com
Asali: UGC

Dalilin mahangurɓar data sha a baki ne, nan take jini ya yanke, to amma sai aka yi coci da ita mai makon akaita asibiti.

Shaidun ido da ido dake zaune a yankin sun ce, koda aka ga jinin yaƙi yankewa ne aka garzaya da ita asibiti inda anan ne ta yanke jiki ta faɗi tare da cewa ga garin ku nan, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

A cewar majiyar tamu:

"Sun samu saɓanin fahimta ne wanda hakan yakai ga faɗa, to amma anyi rashin sa'a matar nan yar garin Ogobiri ta naushe ɗayar matar a waje mai haɗari, hakan yasa ta sheƙa barzahu.

Majiyar tamu ta nisa tare da ɗaukar dogon numfashi ta ƙara da cewa:

"Hmm, mamaciyar ta je ta amshi kuɗin da take bin bashi ne fa. Amma sai wacce ake bi bashi tace bata da kuɗin da zata biya. Nan fa cacar baki ta sarƙe, amma duk da haka sai taje ta ɗauko ₦350 domin ta biya ganin musun yaƙi ƙarewa. Amma mamaciyar da naci taci gaba da kantama mata zagi, ita kuma abin yayi mata ciwo tayi mata mahangurɓa a hanci."

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Yan Bindiga Sun Kutsa Cikin Gidan, Sun Harbe Shugaban Jam'iyya Har Lahira

Koda faruwar lamarin ne, fusatattun matasa suka yiwa ƙauyen Amassoma dirar mikiya sannan suka shiga gidan wacce tayi aika-aikan suka ƙone shi da wuta, a wani salo na ramuwan gayya.

Bayanan dake fita na baya bayan nan sun nuna tuni jami'an tsaro sukai habzi da matasan guda biyu da sukai wannan ƙone ƙonen.

Da aka tuntuɓi kakakin hukumar ƴan sanda ta jihar, Asinim Butswat ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace:

".....Uwar gida Akumere Aregbare, mai shekaru 43 , tabbas tayi faɗa da wata mata mai suna Eniekeduo Atabala, mai shekaru 38 , a garin Ogobiri can kudancin Ijaw, faɗan yayi sanadin mutuwar uwargida Akumere.
“An garzaya da ita babban asibiti na yankin, amma likitoci sun tabbatar da mutuwar ta. Tuni aka yi awon gaba da gawar ta zuwa gidan ajiyar gawa, sanann munyi nasarar kama wacce ake zargi domin ci gaba da bincike.”

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida

Tags: