Gwamnan Jihar Edo Ya Bada Izinin Kama Magabacinsa Adams Oshiomole
- Gwamnatin jihar Edo ta daura alhakin zanga-zangar da aka yi a Edo kan tsohon gwamnan jihar
- Gwamnatin ta bayyana alhininta bisa kona bakunan da akayi da kuma rashin rayuka uku da akayi
- Yan Najeriya na cigaba da fama da wahalar rashin tsabar kudi cikin al'umma tun watan Junairu
Benin City - Gwamnan jihar Edo, Godwin Emefiele, ya umurci jami'an tsaro su damke magabacinsa, Adams Oshiomole, bisa rawar da ake zargin ya taka zanga-zangar da ya haddasa mace-mace da hare-haren bakuna a ranar Laraba.
Akalla mutum uku sun rasa rayukansu kuma an kona bankuna a jihar Edo jiya Laraba sakamakon zanga-zangan karancin Naira da tsadar mai.
Gwamna Obaseki ta bakin kwamishanan yada labaransa, Chris Nehikhare, ya tuhumci tsohon gwamnan jihar Adams Oshiomole, da tunzura yan daba wajen tada zaune tsaye a jihar kan karancin Naira, rahoton Punch.
CBN: Tinubu Ya Gabatar Da Babban Bukata 1 Bayan An Yi Zanga-Zanga Kan Karancin Naira a Fadin Najeriya
Yace:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"Muna cikin gari tun da safe muna tattaunawa da masu zanga-zangar, kuma mun gano akwai lauje cikin nadi."
"Yanzu muna kira ga jami'an tsaro su damke Adams Oshiomole yayi bayani kan abubuwan da ya rika yi cikin Birnin Benin a kwanakin nan. Lallai shi ya tunzura mutane zanga-zanga."
"Na san mutane zasu rika yiwa wannan zanga-zangar ganin rashin kudi ne ya haddasa, amma ko da akwai kamshin gaskiya ciki, yan Najeriya su sani cewa akwai siyasa ciki.
"Saboda da ban mamaki ace jam'iyyar dake da hakkin kawo wannan tsari kuma sune ke tura mutane lalata hotunan kamfen PDP."
Asali: Legit.ng