Dalilai 5 Da Yasa Muka Kawo Tsarin Sauya Fasalin Naira: Buhari Da Safiyar Yau
2 - tsawon mintuna
Shugaba Muhammadu Buhari ya lissafo dalilan da yasa gwamnatinsa ta kawo tsarin sauya fasalin Naira a karshen shekarar 2022.
Buhari ya bayyana hakan ne a jawabin da ya yiwa yan Najeriya da safiyar Alhamis, 16 ga watan Febrairu, 2023.
Ya ce tun da lamarin ya tsananta yanzu, wajibi ne ya bayyanawa yan Najeriya manyan dalilan kawo wannan tsari na sauya fasalin kudi.
Zaku tuna cewa a watan Oktoba 2022, gwamnan bankin CBN, Godwin Emefiele, ya sanar da cewa za'a buga tsaffin takardun N1000, N500 da N200 sannan kuma bayan kwanaki 100 a daina amfani da tsaffi.
Dalilai 5 Da Yasa Muka Kawo Tsarin Sauya Fasalin Naira: Buhari
Shugaba Buhari yace:
"Yanzu ya zama wajibi na sanar da ku dalilan kawo wannan tsari: sun hada da
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
- Bukatar dawo da karfin CBN wajen iko da mulki kan takardun Nairan dake yawo cikin al'umma. A 2015 da muka hau mulki, takardun kudin dake yawo N1.4trillion ne.
- A 2015 adadin kudin dake yawo 78% ne amma yanzu a 2022 ya tashi 85%. Biliyan 500 kadai ke banki yayinda N3.23 trillion ke hannun jama'a. Wannan na taimakawa wajen hauhawar tattalin arziki.
- Adadin kudin dake hannun jama'a boyewa sukayi kuma ba juyawa ba, kuma hakan na kawo koma baya ga tattalin arzikin kasa.
- Shawarin da masana suka bada kan habakan tattalin arziki yasa gwamnati ta yanke shawarar dake mutanen da basu da asusun banki.
- Dubi ga yadda lamarin tsaro yayi tsamari a fadin tarayya, ya zama wajibi gwamnati ta taimakawa jami'an tsaro wajen yaki da biyan fansa da yan bindiga."
Asali: Legit.ng
Authors: