Kwankwaso Kai Mara Hankali Ne, Mai Saka 'Dan Kampan Mata, Kayi Hattara: Fani Kayode
- Tsohon Ministan Sufurin Najeriya ya biyo ta kan dan takarar shugaban kasan jam'iyyar NNPP, Kwankwaso
- Fani Kayode ya nuna bacin ransa bisa jawabin rashin lafiyar da Kwankwaso ya jefi Tinubu da Atiku da shi
- Fani-Kayode ya la'anci Sanata Rabiu Musa Kwankwaso kuma ya kira sa da marasa amfani kuma maras kunya
Diraktan kwamitin masu kare muradun yakin neman zaben jam'iyyar All Progressives Congress APC, a kafafen ra'ayi da sada zumunta na kwamitin Femi Fani-Kayode ya yi dirar Mikiya kan Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso.
Kwankwaso tsohon gwamnan jihar Kano ne, tsohon mataimakin kakakin majalisa, tsohon Ministan tsaro, tsohon Sanata kuma dan takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2023.
Yana takara karkashin inuwar jam'iyyar New Nigerian Peoples Party NNPP.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Fani Kayode ya yi kalamai masu tsaurin gaske kan Kwankwaso a ranar Talata, 27 ga Disamba a shafinsa na Tuwita.
Ya kira Kwankwaso da mutum mara kunya, mara gaskiya kuma matsiyaci.
Wannan ya biyo bayan jawabin da Sanata Rabiu Kwankwaso yayi kan lafiyar yan takarar shugaban kasan jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar da kuma na APC, Asiwaju Bola Tinubu.
Fani Kayode yace:
"Jawabin Kwankwaso cewa: Ba na fitsarin kwance kuma ni ba tayar baya bane."
"Hakane amma ba kada kunya, mara hankali, kuma mara gaskiya. Wadannan mutane biyun da kake zagi sun girmeka nes aba kusa ba, kuma sun fika hankali."
"Hakazalika ba sa sanya wando cikin mata. Kayi hattara.!"
Me Kwankwaso ya fadi
A wani hira da gidan rediyon Alfijir, an yiwa Kwankwaso tambayar wa zai goyawa baya tsakanin Tinubu da Atiku.
Kwankwaso ya yi martanin cewa a cikinsu duka biyu babu wanda ya cancanta saboda daya za'a ga yana fitsari a wando.
Kwankwaso yayi hiran ne yayin ziyarar da ya kai zuwa jihar Katsina.
Kwanakin baya ya yi irinta kan Malam Ibrahim Shekarau
Kwanakin baya, Malam Ibrahim Shekarau yayi jawabi kan lafiyar dan takarar shugaban kasan jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu.
Hakan bai yiwa Fani Kayode dadi ba inda ya yiwa Shekarau tatas har da kiransa matsiyaci,
Fani Kayode ya kira Shekarau a matsayin sha-sha-sha kuma ya ce Allah ya kwashe masa albarka.
Asali: Legit.ng