Bukola Saraki Ya Gargadi Hukumomin Tsaro Kan Batun Gwamnan CBN

Bukola Saraki Ya Gargadi Hukumomin Tsaro Kan Batun Gwamnan CBN

  • Tsohon shugaban majalissar dattijai ya magantu kan turka-turkar gwamnan babban bankin kasa CBN
  • Saraki yace dole ne ayi taka tsan-tsan da abubuwan da suka shafi siyasa da kuma tsaro, kar a maida su wata hanyar amfani a lokacin zabe ko kuma musgunawa wani.
  • Saraki yayi kira da hukumomin gwamnati na tsaro da su san me suke da kuma irin aiyukan da zasu ringa gudanarwa

Abuja: A wata sanarwa da tsohun shugaban majalissar dattijai ya fitar Sen. Bukola Sarki ya shawarci hukumomin tsaron kasar nan kan su kiyaye wajen aikata magu-magu lokacin zabe.

A sanarwa da mai taimakamasa ta kafar yada labarai ya fitar a Abuja tace ya kamata a san takaimame abinda yasa DSS, suke neman kama gwamnan babban bankin sabida kar ai musu gurguwar fahimta, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tarayya Tace Batun Gwamnan Babban Banki Yana Gaban Kotu, Dan Haka Ita Nata Sa Ido

Saraki
Bukola Saraki Ya Gargadi Hukumomin Tsaro Kan Batun Gwamnan CBN Hoto: Daily Post
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Saraki ya roki jami'an tsaron kasar nan da su yi baya-baya da abubuwan suka shafi aiyukan yan siyasa ko zabe, yana mai cewa:

"Kamar ni din nan da aka zarga da daukar nauyin fashi da makamin Offa, aka juya zance aka murda magana, kafin daga bisani kotu ta gano banda laifi ta wanke ni."
"Banji dadi ba sosai kan wannan abu, kuma ina tabbacin irin wannan kan iya sa a samu wani boayyen al'amari ko manakisa wanda ake so a shiryawa wani a lokacin zabe"

Bai kamata Hukumar DSS Ta Sa wa Wasu Rukunin Mutane Takunkumi ba

Cibiyar kula da hada-hadar kudi da kula da tsaftarsa, da bibiyar aiyukan gwamnati CSITT, ta magantu kan yadda hukumar DSS, take sanyawa wasu dokoki da kuma yadda suke son tozarta gwamnan babban bankin kasa

Kara karanta wannan

Munyi Dan Sanin Abinda Mutanen Mu Suka Aikata A Jihar Zamfara - Ministan Buhari

A wata sanarwa da cibiyar ta fitar ta hannun daraktanta tace:

"Rukuni kungiyoyi da suke da rijista a kasashe 164 da suke karkashin wata inuwa sun fito da wani tsari da suka sanya masana a ciki da zai kula da hada-hadar kudade da kuma masu diban kudaden ba bisa ka'ida ba zasu iya dakatar da Nigeria a ciki muddin aka kama gwamnan Babban banki

Cibiyar CNPP da takaarta ta CSOs sun fitar da wata sanarwa mai kama da wannan da take cewa muddin ba'ai bincike akan wannan turka-turkar ba akwai matsala babba da kasashen da suke mu'amala da Naira zasu ja baya ko dauakan mataki

Bisa ga wannan batun gwamnan da yaki ci yaki cinyewa ne dai majalissar kasa ta amincita ta saurari mataimakiyar gwamna Hajiya Aisha Ahmed da ta wakilce a jin ba'asin abinda yake zuwa ya ke komowa, da kuma batun kayyada cire kudi Dubu N100,000 a sati ga dai-daikun mutane

Kara karanta wannan

Rudani: Tinubu ya hada kura, bidiyo ya nuna lokacin da yake ba wani dattijo tsabar kudi

Duk Wannda Yake Son Dorewar Dimukuradiyya To Dole Ne Ya Bi Doka Da Oda

A lokuta mabanbanta Dimukuradiyya wata dama ce ga duniya gaba dayanta, dole ne muga yadda Nigeria zata ci gaba.

Kamar yadda muke da yawa kuma muke da arziki ya kamata ace munyiwa kanmu fadan ta nustu wajen gudanar da aiyukanmu da kiyaye doka da oda.

wannan batutuwan na zuwa ne yayin da dan gwagwarmaya Lord Hannan ke magana kan batun gwamnann baban bankin kasa CBN, yace Ya kamata abi batun nan a hanakali a samo bakin zaren.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida