Duk Wanda Ya Kuskura Ya Shiga Wani Magu-Magu Zai Kare A Kurkuku - NYSC Ga Yan Bautar Kasa
- Duk Wanda Ya Kuskura Ya Shiga Wani Magu-Magu Zai Kare A Kurkuku - NYSC Ga Yan Bautar Kasa
- Tun shekarar 2011, hukumar zabe da hukumar yiwa kasa hidima ke hada hannu da gwiwa dan gudunar da zabe tare da membobin NYSC, din
- A bana ma dai hukumar ta hada hannu da INEC, wajen gudanar da zaben kamar yadda aka gani a jihohin Osun da Ekiti
Abuja: Hukumar kula da masu yiwa kasa hidima (NYSC) ta gargadi masu yiwa kasa hidima kan shiga cikin duk wani nau’i na magudin zabe a babban zabe mai zuwa. Rahotan Daily Trust
Mukaddashin Darakta-Janar na NYSC, Misis Christy Uba, itace tai wannan gargadin yayin ziyarar aiki da ta kai sansanin horar da masu yiwa kasa hidima a Amada a karamar hukumar Akko.
Tace duk memban da aka samu da hannu wajen aiwatar da wani magu-magu na zabe to ya sani zai kare ne a gaban kuliya ko kuma gidan yari.
Ta ce shirin na NYSC ya taka rawar gani wajen gudanar da zabe a kasar nan tsawon shekaru tare da hadin gwiwar hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC).
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Uba ta kara da cewa duk memban da aka samu da hannu a kowane irin laifin zabe zai fuskanci fushin doka kamar yadda dokar zabe ta 2022 ta tanada.
Ta ce,
"Tunda ya zama dole ne su kasance a aiyukan hukumar zabe, to kamata yai ace kun tsaya a tsaka-tsaki ba tare da goyan bayan wata jam'iyya ba, sannan suyi aiki da kishi da kuma san kasa".
Jami'an Rundunar Tsaron Farin Kaya DSS, Sunyi Gaba Da Babban Dalibin Abdul-Jabbar Sabida Sabawa Dokar Zaman Kotu
“Idan ka karya doka, za a yi maka kamar kowane dan Najeriya. Babu saussauci ga mambobin hukumar; duk lokacin da aka ji wani daga cikin membobin hukumar nan ya saci akwati ko takardar kada kuri'a to ya sani zai kare a gidan yari.”
Asibitocin Sansanin Yan Yiwa Kasa Hidima Na Cikin Tsaka mai Wuya
A wani labarin kuma mukaddashin daraktan ta musanta zargin cewa asibitocin da ke wasu sansanonin a kasar ba su da kayayyakin kiwon lafiya, tana mai cewa
" A ko da yaushe ana ba da fifiko ga dukkan mambobin kungiyar a fadin kasar."
“Ciyarwarsu, lafiyarsu, da walwalarsu ba abu ne mai sauki ba; muna hada kai da Hukumar Inshorar Lafiya ta Kasa (NHIS) kuma zan iya gaya muku a koyaushe ana samar da magunguna,” in ji ta.
An Yi Kira Da Masu Yiwa Kasa Hidima Su Zama Na Gari
A wani labarin mai kama da wannan hukumar tayi kira da membobinta su zama 'yan kasa na gari wajen tabbatar da kishi da kuma san kasa gaba da komai.
Wannan kiran na zuwa ne bayan da Mukadashin shugaban Hukumar Mrs. Uba ta ziyarci sansanin 'yan bautar kasa a garin Ibadan da ke jihar Oyo kamar yadda Radio Nigeria Ibadan ta rawaito.
Asali: Legit.ng