Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Yankewa AbdulJabbar Kabara Hukuncin Kisa

Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Yankewa AbdulJabbar Kabara Hukuncin Kisa

  • Bayan zama 30 da akayi tun bayan sama da shekara guda ana yi, an yanke hukunci kan Sheikh AbdulJabbar
  • Gwamnatin jihar Kano ta gurfanar da Malamin gaban kotun shari'a bisa zargin batanci kan manzon Allah
  • Alkali ya baiwa Malamin damar daukaka kara cikin kwanaki Talatin kafin a zartar da hukuncin

Kano - Bayan sama da shekara daya ana kai ruwa rana a kotun shari'a dake jihar Kano, an zo karshe a yau Alhamis, 15 ga watan Disamba, 2022.

Alkalin kotun ya karanto jerin laifukan da kotu ta kama Malam Abduljabbar da su kuma ya yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Mai shari'a Sarki Yola ya tabbatar da duk maganganun da Abduljabbar yake yi shi ya kirkira kuma ya jinginawa ma'aiki (SAW).

Mai shari'a ya tabbatar da cewa maganganun fassara hadisan manzon Allah da Abduljabbar yace kage ne ko jingina ne, karya yake kuma hasali ma shine ya jingina kalmomin ga Ma'aiki.

Kara karanta wannan

Kaico: Dan Hisbah ya yi babban laifi, Kotun Kano ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya

AbdulJabbar
Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Yankewa AbdulJabbar Kabara Hukuncin Kisa
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar Alkali:

Sashi na ɗati uku da sittin da uku sashin (f) ya bada hukunci haka:
An yankewa Abduljabar hukuncin kisa Ta hanyar rataya
Sashi 380 ne ya bada wannan hukuncin ta hanyar rataya
Kuma kotu ta kwace litttafansa da ya gabatar da su a gaban kotu dan sheda
Kuma kotu ta bada umarnin kwace masallatansa gudu biyu Na filin Mushe dana Unguwar sabuwar Gwandu

Alkalin ya kara da cewa Kotu ta umarci hani da saka karatunsa a Gidajen radio, Gidajen Talabijin Da kafafen sadarwa.

Hakazalika Kotu ta bashi damar daukaka kara nan da kwana 30.

AbdulJabbar ya ce Alkali karya yake masa

Sheikh Abduljabbar Kabara, gabanin yanke masa hukunci ya fara fadawa Alkali kotun maganganu kuma yace alkali karya yake masa.

Ba tare da bata lokaci ba jami'ai suka dakatar da shi daga maganganun kuma aka tafi hutu.

Kara karanta wannan

Kano: Alkali ta Yankewa Aisha Hukuncin Kisa ta Hanyar Rataya kan Kisan Bahijja

Wakilin Legit dake kotun yace:

"Shari'a ce da za'a iya cewa tazo karshe tun da an riga an tabbatar da zarge-zargen da ake yiwa shi wanda gwamnati ta shiga kara kan zargi da kuma abubuwan da ake masa"
Abinda kowa ke fada daga bakin yan jarida shine yadda shi Abduljabar din ya fada wa alkali maganganu.
Kuma ya nuna baya neman ko wanne irin sassauci daga wajen Alkali."

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida