Abin Alajabi: Matar Da Ta Haifi Yan Tara Ta Tawo Gida Abinda Ba'a Taba Samu Ba

Abin Alajabi: Matar Da Ta Haifi Yan Tara Ta Tawo Gida Abinda Ba'a Taba Samu Ba

  • Ma'auranta 'yan kasar Mali, Halima Cissé da mijinta Kader Arby, sun aje tarihin da ba'a taba yi a duniya ba.
  • Jariran Halima Cissé sun karya kundin tarihin duniya na Guinness na mafi yawan yaran da aka haifa a cikin haihuwa guda wanda suka rayu.
  • ‘Yan matan biyar da maza hudu an haife su ne ta hanyar yiwa mahaifiyar tasu tiyata kuma daga karshe sun koma Mali, kasarsu ta haihuwa

Mali: 4 ga Mayu, 2021, za ta kasance har abada a cikin zukatan wasu ma'aurata 'yan Mali waɗanda suka dau hankalin duniya bayan haihuwar jariransu tara a lokaci ɗaya.

Uwa ta ja hankalin duniya

Duk ba burin Halima Cissé da mijinta Kader Arby su dau hanakalin duniya saboda yadda ba ya cikin tsarinsu, amma ya zasu yi tunda suna tare da sojojin kasar mali.

Kara karanta wannan

Elon Musk ya Saka Gadaje a Ofisoshi Twitter, Ya Ja Kunne Kan Sharholiya Babu Aiki Tukuru

Babu shakka haihuwa ce ta musamman yayin da aka haifi jarirai tara ta hanyar tiyata kuma wacce ta kasance cikin sauri. Rahotan legit.ng

Yan Tara
Abin Alajabi: Matar Da Ta Haifi Yan Tara Ta Tawo Gida Abinda Ba'a Taba Samu Ba Hoto: Peter Allen
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Haihuwa a Maroko

Lokacin da aka ga halin da take ciki, kuma likitocin Mali basu iya ba, sai suka kwantar mata da hankali sannan suka kaita kasar Maroko dominta samu kulawa ita da ‘ya’yanta.

Likitocin sun yi amanna cewa jariran bakwai ne kuma sun firgita a lokacin da adadinsu ya kai tara a ranar da za a yi mata tiyatar.

Bayan haihuwar, mahaifiyar da 'ya'yanta 9 suna zaune a wani gidan shakatawa.

Gidan shakatawa na Morroco

Bayan haihuwar sun zauna a wani gidan shakatawa da ke ƙasar Maroko domin a kula da su yadda ya kamata da kuma kulawar likitoci da ma’aikatan jinya.

Kara karanta wannan

Emefiele Yana Amfani Da Matsayinsa Don 'Azabtar' Da Yan Siyasa, Gwamnan Arewa Mai Karfin Fada Aji Ya Yi Zargi

Arby, mahaifinsu yakan komawa Mali dan kula da 'yarsu ta fari Soda, wacce ta kasance a gida a Timbuktu lokacin da aka fitar da Cissé.

Mahaifiyar 'ya'ya goman ba tayi tunanin haka rayuwarta za ta kasance mata ba.

Gwamnatin Mali ta aike da wata tawaga domin tarbar Uwar da taimaka mata wajen shiga da saukan ababen hawa.

A wata wayar tarho da sukayi ran Lahadi, Disamba 11, 2022, ma'auratan sun gaya wa Daily News UK cewa:

"Mun yi matukar farin ciki da samun damar komawa kasar Mali tare."

Bayan tarbar ta a kasar Mali, Mahaifiyar ta karbi takardar shaida daga "Guinness Book of Records".

Yan Taraaaa
Abin Alajabi: Matar Da Ta Haifi Yan Tara Ta Tawo Gida Abinda Ba'a Taba Samu Ba Hoto: Peter Allen
Asali: UGC

Bayan Shafe shekaru tana jira, Wata Mata Ta Haihu

A wani labarin mai kama da wannan, Legit.ng ta rawaito cewa wata ‘yar Najeriya, Ogechi Emmanuel, a ranar Laraba, 22 ga watan Satumba, 2021, ta bayyana cewa ta haifi tagwaye a shafin facebook.

Kara karanta wannan

Muna tare da CBN kan dokar kayyade cire kudi: Kungiyar Matasa

Ogechi ta bayyana cewa ta haihu ne bayan da ta shafe shekaru tara da auren ta, ba tare da samun haihuwa ba

Ta kara da cewa Allah ya bata tagwaye. sannan, ta yi addu'a ga duk waɗanda suke son samun haihuwa Allah ya basu.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida