Shugaba Muhammadu Buhari Ya Kaddamar Da Sabon Kudin Najeriya

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Kaddamar Da Sabon Kudin Najeriya

  • Bayan wata guda ana tsamanni da sauraro, sabbin takardun kudin Najeriya Naira sun bayyana
  • Sama da shekaru 15 kenan da sauya fasalin kudaden naira N10, N20, da N50 da akayi a 2007
  • Gwamnan CBN ya sanar da cewa an kara alkaluman kudin ruwa daga 15.5% zuwa 16.5%

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana samfurin sabon kudin Najeriya 'Naira' yau Laraba, 23 ga Nuwamba, 2023 a fadar shugaban kasa, Aso Rock Villa, Abuja.

Shugaban kasan ya bayyana kudaden ne a taron majalisar zartaswa FEC da ke gudana kowace Laraba.

Daga cikin wadanda suka halarci zaman akwai manyan jami'an fadar gwamnati, ministoci da gwamnan babban bankin Najeriya CBN.

Hakazalika akwai shugaban hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau EFCC, Mr AbdulRasheed Bawa.

Kara karanta wannan

Mene ne Gaskiyar Lamarin? Bidiyon Sabbin Takardun Naira da Aka Canzawa Fasali Ya Bazu

Sabon kudi
Shugaba Muhammadu Buhari Ya Kaddamar Da Sabon Kudin Najeriya Hoto: @NigeriaGov
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sabon Naira
Shugaba Muhammadu Buhari Ya Kaddamar Da Sabon Kudin Najeriya Hoto: @NigeriaGov
Asali: Twitter

Mun kawo muku cewa Emefiele a ranar 26 ga Oktoba ya sanar da sauya fasalin takardun Naira N200, N500, da N1000.

Yace za'a fitar da sabbin takardun ranar 15 ga Disamba, 2022 kuma za'a daina amfani da wadanda ke gari yanzu ranar 31 ga Junairu, 2023.

Amma, Emefiele yace gwamnati ta canza shawara, ba za'a jira sai ranar 15 ga Disamba ba saboda Shugaban kasa na bayyanasu ranar Laraba zasu fara yawo.

N1000
Shugaba Muhammadu Buhari Ya Kaddamar Da Sabon Kudin Najeriya
Asali: Facebook

Buhari da sabbin kudi
Shugaba Muhammadu Buhari Ya Kaddamar Da Sabon Kudin Najeriya
Asali: Twitter

Dalilan sauya fasalin Naira uku, a cewar shugaba Buhar

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa babu ja da baya game da lamarin sauya fasalin takardun kudin Najeriya 'Naira'.

Buhari ya bayyana hakan yayinda yake hira da manema labarai a Landan.

Yace Tattalin arzikin Najeriya zai amfana da wannan abu saboda wadannan dalilai guda uku:

Kara karanta wannan

"Kowa A Jiha Ta Masoyin Buhari Ne": Gwamnan PDP Ya Aika Saƙo Mai Kaɗa Hanta Ga Atiku

- Hauhawar farashin kaya zai ragu

- Masu hada kudaden jabu zasuyi asara

- Kudaden da yawo a gari zasu ragu

Gwamnan CBN Emefiele Ya Umurci Dukkan Bankuna Su Fara Budewa Ranar Asabar

Gwamnan Babban Bankin Najeriya CBN, Godwin Emefiele ya umurci dukkan bankunan dake Najeriya su fara budewa ofishohinsu ranakun Asabar daga yanzu zuwa ranar 31 ga Junairu don mutane su samu damar mayar da kudadensu.

Diraktan Yada Labaran Bankin, Osita Nwasinobi, ne ya sanar da wannan umurni da aka yiwa bankunan.

Ya bayyana hakan ne a wani taron baja kolin CBN da ya gudana ranar Alhamis a Ilori, birnin jihar Kwara.

Nwasinobi ya samu wakilcin mukaddashin Diraktan sadarwan bankin, Akpama Uket.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida